Yadda Buhari Ya Tsiyata Najeriya Kafin Mikawa Bola Tinubu Mulki Inji Nuhu Ribadu
- Mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro ya ce Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a wani irin mawuyacin hali
- Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa gwamnatinsu ta na biyan bashin abin da ya faru ne a gwamnatin baya
- Hadimin shugaban Najeriyan ya koka game da yadda aka damkawa Shugaba Tinubu ragamar kasar a tsiyace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya fito ya nanata cewa Muhammadu Buhari ya tsiyata kasa.
A wajen wani taron sojoji na shekara-shekara da aka shirya, This Day ta ce Mallam Nuhu Ribadu ya nuna sun karbi mulkin gwamnati a tsiyace.
Hadimin shugaban kasar ya ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya karbi ragamar mulki ne bayan an tsiyata kasa, babu komai cikin baitul-mali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nuhu Ribadu wajen taron sojoji
Ribadu ya fada a wajen taron cewa gwamnatin tarayya ta na biyan bashin abin da aka dauko ko aka dauke a lokacin gwamnatin da ta shude.
A cewar NSA din, gwamnatin Bola Tinubu tana fama da kalubale sosai na rashin kudi.
Abin da NSANuhu Ribadu ya fada
"Muna fuskantar cikas sosai wajen kasafin kudi. Zai yi kyau in fada maku. Zai yi kyau ku sani. Mu na cikin halin ha’ula’i.
Mun gaji kasa mai wahalar sha’ani, kasa a tsiyace har ta kai mu na biyan bashin abin da aka dauka. Abin ya yi kamari.
Amma gwamnatin nan ta na yin bakin kokarinta wajen ganin mun sauke nauyin da ya rataya, daga ciki har da na sojoji."
- Nuhu Ribadu
Su wa aka gani a wajen taron a Abuja?
Daily Trust ta ce Ministocin tsaro; Mohammed Badaru, Bello Matawalle da shugaban hafsun tsaro, Janar Christopher Musa sun halarci taron.
Sauran wadanda su ka je wajen taron sun hada babban sakataren ma’aikatar tsaro, Ibrahim Kana da sauran manyan jami’an sojojin kasar.
An shiga yajin-aiki a Najeriya
Ana da labari cikin tsakar daren kungiyoyin NLC da TUC su ka shiga yajin-aiki a ko ina a fadin kasar nan, hakan zai kara jagwalgwala tattalin arziki.
Abin da ya fusata ma’aikatan Najeriya shi ne ba a cafke wadanda su ka doke Festus Osifo ba bayan an lakadawa Shugaban NLC duka a Imo kwanaki.
Asali: Legit.ng