Tashin Hankali a Abuja Yayin da Tayar Jirgi Ta Cije Yana Tsaka da Tafiya Bayan Sauka a Tasha
- Jirgin sama ya samu tsaiko yayin sauka a filin jirgin saman Babban Birnin Tarayya Abuja, inji rahoto
- An bayyana cewa, ba a samu mutuwa ko rauni ba, amma ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin
- Ya zuwa yanzu, an ce tayar jirgin ne ta makale a ciyarwar da ta mamaye wani yanki na titin saukar jirgi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja - An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja biyo bayan tsaikon da aka samu tare da jirgin Aerocontractors.
An ruwaito cewa, jirgin da ke zirga-zirgar Legas-Abuja ya sauka a sashe na A4 a filin jirgin, inda tayarsa ta cike ta makale a filin jirgin, Daily Trust ta ruwaito.
Yakar Falasdinawa da Isra'ila ke yi: Ayarin farko na motocin agaji daga daular Saudiyya sun isa Gaza
Sai dai, rahotannin da ke iso mu sun bayyana cewa, ba a samu rauni ko mutuwa ba, kuma an yi nasarar kwashe fasinjojin jirgin kana an fara aikin cire jirgin a hanyar da ya sauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar bincike da kula da lafiyar jiragen sama (NSIB) ta fara bincike kan lamarin bayan da aka sanar da ita yanayin da ake ciki.
Wane jirgi ne hakan ta faru dashi?
Jirgin da hakan ta faru dashi shi ne Boeing 733 mai lamba 5N-BYQ na kasa da rajista, kuma hakan ya faru ne da misalin karfe 10:47 na safe a ranar 12 ga Nuwamba, 2023., rahoton Vanguard.
Daraktan hulda da jama’a na NSIB, Dokta James Odaudu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce:
“Jirgin da ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja daga Legas kuma a kokarinsa na fita daga titin A4 ya cije a cikin ciyawar da ta mamaye titin.
“Saboda haka, an rufe titin jirgin har zuwa lokacin da za a janye jirgin daga titin. Babu wani rauni ko mutuwa.
"Don hka NSIB na neman bayanai daga jama'a kamar dai hotuna, bidiyo ko rikodin shaida don taimakawa wajen gudanar da cikakken bincike."
Hadarin jirgi da ministan Tinubu
An bayyana yadda wani jirgin sama da ke dauke da fasinja ya samu tsaiko a wani yankin Ibadan na jihar Oyo.
A cewar majiya, an ce akwai daya daga ministocin Shugaba Tinubu a cikin jirgin, lamarin da ya dauki hankalin jama'a a sosai.
Ya zuwa yanzu, an ce jirgin bai hallaka kowa ba, ana ci gaba da bincike kan yadda za a kaucewa hakan a gaba.
Asali: Legit.ng