Yakar Falasdinawa da Isra’ila Ke Yi: Ayarin Farko Na Motocin Agaji Daga Daular Saudiyya Sun Isa Gaza

Yakar Falasdinawa da Isra’ila Ke Yi: Ayarin Farko Na Motocin Agaji Daga Daular Saudiyya Sun Isa Gaza

  • Kasar Saudiyya ta kai agajin gaggawa ga mazauna Gaza yayin da Isra'ila ke ci gaba da kisan gilla a kasar
  • An kashe Falasdinawa da yawa a hare-haren bama-bamai da sojojin Isra'ila ke kaiwa kan mazauna Gaza
  • Yakin ya fara ne yayin da Hamas ta kai hari kan Isra'ila, wanda Isra'ila ta gagara kaiwa ga Hamas, har ya zuwa yanzu

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Kasar Saudiyya - Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ba da rahoton cewa, ayarin farko na motocin agajin da cibiyar ba da agaji ta Sarki Salman ta aike zuwa Gaza sun tsallaka kan iyakar Rafah zuwa yankin a jiya Lahadi.

Tallafin na jin kai wanda ya hada da kayan abinci da matsuguni, wani bangare ne na tausayawa daga kasar Saudiyya ga Falasdinawan Gaza.

Kara karanta wannan

A karshe, Shugaba Tinubu ya Tsoma baki, ya faɗi matsayar Najeriya kan yakin Isra'ila da Falasɗinu

Kayan agaji daga Saudiyya sun isa Gaza
Kayan da Saudiyya ta tura Gaza | Hotuna: arabnews.com, reuters.com
Asali: UGC

An ruwaito cewa, an kaddamar da shirin ba da agajin ne a karkashin jagorancin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a farkon wannan wata, Arab News ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin saman agaji ya isa Gaza

A halin da ake ciki kuma, wani jirgin agaji na hudu na Saudiyya dauke da kayan agaji daga Masarautar zuwa Gaza ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na El-Arish na kasar Masar a ranar Asabar.

Shirin dai ya yi daidai da dadewar da Saudiyya ta yi tana tallafawa al'ummar Palasdinawa a lokutan rikici da addabar da Isra'ila ke yi musu a lokuta masu tsawo.

Idan baku manta ba, Falasdinawa na fuskantar hare-haren kare dangi da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa daga sojin Isra'ila, rahoton Saudi Gazette.

A wannan karon, an kashe Falasdinawa masu yawa, wadanda mafi yawancinsu yara ne da mata da basu da alaka da yakin da Isra'ila ke yi da sojin Hamas.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

UNICEF ta koka kan kisan yara da Isra'ila ta yi a Gaza

A tun farko, hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Lahadi cewa rayukan akalla jarirai 120 da aka haifa a asibitocin Gaza ne ke cikin hadari yayin da aka toshe hanyoyin shigar man fetur yankin, rahoton Channels Tv.

Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Lahadi cewa rayukan akalla jarirai 120 da aka haifa a asibitocin Gaza ne ke cikin hadari yayin da aka toshe hanyoyin shigar man fetur yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel