Manoma na Biyan ‘Yan Bindiga Kudi Kafin Su Iya Girbe Amfanin Gonarsu a Kaduna
- A wasu kauyuka da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, manoma suna wahala da miyagun ‘yan bindiga
- Wadanda su ka yi noma a shekarar nan ba su tsira ba, dolensu su ke ba ‘yan bindiga kudi kafin su iya yin girbi
- Duk manomin da aka samu ya yi taurin kai, zai iya rasa rayuwarsa ko kuwa miyagun su dauke kayan gonan
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - A jihar Kaduna, lamarin rashin tsaro ya kai yanayin da mutane su na cire kudi daga aljihunsu, suna mikawa ‘yan bindiga.
Abin da ya sa hakan ta ke faruwa kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto shi ne, mutane na so a cire kayan amfani daga gonaki.
‘Yan bindigan da su ka addabi kauyukan Giwa suna tursasawa manoma biyan kudi idan suna sha’awar girbe abin da su ka noma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun addabi manoman Kaduna
Manoman da ke zaune a kauyuka irinsu Kidandan da Galadimawa suna cikin masu biyan kudi domin su iya yin aiki a gonakinsu.
A Angular Fala’u da Kerawa kuwa, rahoton ya ce a yanzu manoman da ke kauyukan nan ba su iya shiga gonakinsu hankali kwance.
An saba dauke manoma a wadannan kauyuka, a nemi ‘yanuwansu su biya kudin fansa, ba yau aka fara wannan a jihar Kaduna ba.
Wani mazaunin Kidandan, Malam Jamil Kidandan ya bayyana cewa mutane su kan biya N70, 000 da N100, 000 kafin su iya yin girbi.
Sai manomi ya ba ‘yan bindiga wadannan kudi sannan zai cire abin da ya shuka a gona a lokacin da ake ta wayyo da farashin hatsi.
Idan manomi ya ki biyan kudin fa?
Wanda bai biya kudin ba sai gamu da dayan abububuwa uku; ayi garkuwa da shi, a kashe shi ko ‘yan bindiga su dauke kayan gonarsa.
Miyagun ‘yan bindigan suna gefe, manomi zai yi magana da yaransu, a yanke farashin da zai biya kafin ya shiga gonar da ya noma.
Kauyawan sun ce daga cikin ‘yan bindigan da su ka addabi yankin Galadimawa akwai Buhari da yaransa irinsu Gana’i da Kwalameri.
Za a ga karin tsadar rayuwa
Wani shugaban al’umma Malam Jafar Anaba da aka fatattaka daga kauyen Anguwar Salahu ya ce za a iya yin wahalar abinci a shekarar nan.
Ana da labari abubuwa za su kara tsada yayin da sabon tsarin da bankin CBN ya fito da shi, yake cigaba da tasiri ga tattalin arzikin kasa.
Baya ga karyewar kudin gida da tashin Dala, an cire tallafin fetur kuma dizil ya yi tsada, yanzu kuma kwastam sun kara kudin kawo kaya.
Asali: Legit.ng