Shugaba Tinubu Zai Cigaba da Biyan Tallafi, Ya Ki Yarda a Kara Kudin Wutar Lantarki
- Gwamnatin tarayya ba ta da niyyar yin kari a kan kudin shan lantarki saboda matsin lamba da tsadar rayuwa da ake ciki
- Ministan wutar lantarki ya shaida cewa a yanzu farashi ba zai canza ba, ya tabbatar da cewa gwamnati na biyan tallafi
- Kafin kudi ya canza, Adebayo Adelabu ya nuna akwai bukatar a wayar da kan jama’a kuma karfin lantarki ya karu a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Duk da kiraye-kiraye da ake yi na karin kudin shan wutar lantarki a Najeriya, a ranar Laraba gwamnatin tarayya ta ce ba za ayi haka ba.
Tribune ta rahoto gwamnatin tarayya ta na cewa halin tattalin arzikin da kasa ta ke ciki yau, ba zai bari a kawo karin kudin wutan lantarki ba.
A wajen wata zantawa da ya yi da manema labarai a ranar Laraba, Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya ce shakka babu akwai bukatar ayi kari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudin wutar lantarki zai iya ribanya
Amma duk da haka, Cif Adebayo Adelabu ya nuna gwamnati ba za ta amince da karin ba wanda zai jawo kudin da mutane su ke biya ya nunku.
A cewar Mai girma Ministan, tun tuni ya kamata gwamnatin tarayya ta yarda a sauya farashin, amma halin siyasa da tausayi ya hana ayi hakan.
"Babu dabara a siyasa a dabbaka karin farashin a yanzu wanda kusan zai ribanya kudin da ake biya a halin yanzu.
Ba na tunanin wannan abu ne da za mu iya yi nan take."
- Adebayo Adelabu
Yaushe farashin lantarki zai tashi?
Punch ta ce Ministan ya nuna kafin a iya yin karin kudin shan wutan, dole sai an wayar da kan al’umma kuma a tabbata wutar kasar ta karu.
Tashar Zungeru za ta fara aiki nan da Disamba, duk da haka Ministan ya ce abin kunya ne idan aka duba cewa megawatta 4000 ake iya samu.
Yadda ake karin kudin lantarki
Tsarin MYTO ya bada dama a rika duba kudin wuta sau biyu a shekara la’akari da tashin farashin kaya, canjin darajar Naira da kuma wasu dalilan.
Duk bayan shekaru biyar ana duba lamarin da nufin a canza farashin da ake saida wuta. Har yanzu gwamnatin tarayya ta na biyan tallafin wuta.
NERC ta yi karin kudin lantarki
Kwanaki aka ji labari NERC za ta yi zama na musamman da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan karin kudin wuta kamar yadda aka saba.
Hukumar NERC ta ce kamfanonin DisCos 11 sun nemi su canza farashin da ake saida lantarki lura da cewa Dala ta koma fiye da N785/$1 daga N400/$1.
Asali: Legit.ng