Satar Mazakuta: Tsagera Sun Yi Wa Lakcara Dukan Kawo Wuka a Jihar Arewa, ’Yan Sanda Sun Fusata
- Wani lakcara ya tsira da kyar a Makurdi babban birnin jihar Benue bayan matasa sun yi ma sa dukan kawo wuka
- Matasan na zargin Dakta Emmanuel Aime na Kwalegin Akawe Torkuta da ke birnin da zargin satar mazakutar wani matashi
- Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Catherine Anene ta yi Allah wadai da hukuncin matasan
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue – Wasu tsagera sun yi wa lakcara dukan tsiya a jihar Benue kan zargin satar mazakuta.
Lakcaran mai suna Dakta Emmanuel Aime na Kwalegin Fasaha ta Akawe Torkula da ke Makurdi ya gamu da tsautsayin ne bayan matasan sun zarge shi.
Mene ake zargin lakcaran a kai?
Lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba 8 ga watan Nuwamba a Makurdi babban birnin jihar Benue, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shaidan gani da ido ya cewa an zargi lakcaran ne bayan wani matashi ya yi korafin kan batar mazakutarsa.
Ya ce ya na korafin kenan sai ya nuna lakcaran mai matsakaicin shekaru wanda ya zo wucewa.
Wane martani ‘yan sanda su ka yi?
Nuna shin ke da wuya matasan su ka nufo wurin da lamarin ya faru tare da ma sa dukan tsiya, cewar Newstral.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Catherine Anene ta yi Allah wadai da hukuncin matasan.
Anene ta ce rundunar su yanzu haka sun yi nasara cafke mutane biyu da ake zargin da hannunsu a ciki.
Ta ce:
“Abin kunya a wurin wasu mutane, ba su mutunta doka kwata-kwata a rayuwarsu bare wani, ta yaya hakan zai faru a wannan zamanin?
“Mun yi nasarar cafke wasu mutane biyu da hannu a cikin wannan ta’asa kuma za su fuskanci hukunci mai tsanani.”
Ta ce ya kamata malaman addinai da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma su shia fada da irin wannan, ya kamata mu ilmantar da mutane.
Matasa sun daka Fasto kan satar mazakuta
Kun ji cewa, matasa sun yi wa wani Fasto dukan tsiya kan zargin satar mazakuta.
Wannan na zuwa ne bayan wani matashi ya yi korafin batar mazakutarsa a wurin da lamarin ya faru.
Asali: Legit.ng