Zaben Imo 2023: Jerin Sunayen Gwamnonin Jihar Imo Daga 1999 Zuwa Yanzu

Zaben Imo 2023: Jerin Sunayen Gwamnonin Jihar Imo Daga 1999 Zuwa Yanzu

Jihar Imo za ta sake fuskantar wani sauyin siyasa, a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, a lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta sake gudanar da wani zaben gwamna a jihar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin Gwamna Hope Uzodinma zai zo karshe a watan Janairun 2024, kuma ana sa ran za a bude wani sabon babi na rayuwa a jihar.

An kafa jihar Imo ne a ranar 17 ga Maris 1976 a zamanin gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin daga yankin jihar Kudu maso Gabas. Tun daga lokacin da aka kirkireta, jihar ta samu shugabanci na soja da na dimokradiyya.

Imo 2023/Tsoffin Gwamnonin Jihar Imo/Rochas Okorocha/Hope Uzodinma/Emeka Ihedioha
Duba cikakken jerin sunaye da bayanan tsoffin gwamnonin jihar Imo Hoto: Rochas Okorocha, Hope Uzodinma, Emeka Ihedioha
Asali: Twitter

Sai dai tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, jihar ta samu 'yanci na tsarin dimokuradiyya ta hanyar gudanar da zabe da yanke hukunci na kotu.

Kara karanta wannan

Zan gina mu ku otal a kan ruwa, dan takarar gwamna a jihar Kogi ya yi alkawari, ya fadi dalili

Ga jerin gwamnonin dimokuradiyya na Imo daga 1999:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Achike Udenwa

Udenwa ya zama gwamnan jihar Imo ne bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a Najeriya a shekarar 1999 a karkashin jam'iyyar PDP.

An sake zabar shi a karkashin jam'iyyar a zaben 2003, kuma wa’adinsa ya kare a shekarar 2007. An haife shi a shekarar 1948.

Ikedi Ohakim

Ohakim ya gaji Udenwa a zaben gwamna a 2007 a jihar Imo a karkashin jam’iyyar Progressive Peoples Alliance (PPA). Daga baya ya koma jam’iyyar PDP amma ya kasa samun damar komawa kan kujerar gwamnan jihar a karo na biyu sakamakon kayen da ya sha a zaben 2011.

A farkon shekarar nan ne tsohon gwamnan ya ji a jikinsa illar rashin tsaron da ya addabi jihohin Kudu maso Gabas biyo bayan wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba su ka kai masa farmaki a yankin, amma ya tsallake rijiya da baya, kamar yadda rahoton jaridar The Punch ya nuna.

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

Rochas Okorocha

Okorocha ya doke Ohakim a zaben gwamna na 2011 kuma ya yi wa'adin mulki biyu a jere kafin ya koma majalisar dattawa a 2019.

Ya kasance daya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da ke da tsaurin ra'ayi, wanda kuma hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ke yawan bibiyarsa jim kadan bayan sauka daga mulki.

Emeka Ihedioha

Ihedioha ya gaji Okorocha a matsayin gwamnan jihar Imo a karkashin jam’iyyar PDP, amma bai jima akan mulki ba, sakamakon wasu shari’o’in kotu da magudin zabe da suka kawo wa nasarar zaben sa cikas.

Bayan doguwar takaddamar shari’a tsakaninsa da abokin hamayyarsa daga jam’iyyar APC, All Progressives Grand Alliance (APGA), da sauran su, kotun koli ta tsige Ihediora a watan Janairun 2020, hukuncin da ya sha suka sosai.

Hope Uzodinma

Uzodinma shi ne gwamnan jihar Imo na yanzu kuma yana neman tazarce a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

APC, PDP, LP: An yi hasashen makomar Gwamna Uzodimma a zaben ranar Asabar

Gwamnan ya sha kaye a hannun Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP a zaben 2019 kuma ya zo na hudu a zaben, amma ya samu nasarar zama gwamnan jihar bisa hukuncin kotu.

Nasarar da Uzodinma ya samu a kotun ya sha suka daga Mai shari’a Musa Dattijo Muhammad na kotun koli (mai ritaya), wanda ya koka da yadda tsarin shari’ar Najeriya ke tabarbarewa, inda ya bayyana nasarar da gwamnan jihar Imo ya samu a kotun koli a matsayin shari'ar da ya kamata a zauna ayi nazari kanta.

Uzodinma ne zai lashe zaben gwamnan Imo a 2023

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda aka yi hasashen cewa Gwamna Hope Uzodinma shi ne zai lashe zaben gwamnan jihar Imo da za a gudanar ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Chizorom Ofoegbu, wani mai fashin baki kan al'amuran siyasa da aka fi sani da 'Ijele Speaks', yayi wannan hasashen yayin da ya ke tsokaci kan zaben jihar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.