Matsala Ta Tunkaro, Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Kira Babban Taron NEC Kan Wasu Batutuwa
- Ƙungiyar kwadago NLC da takwararta TUC sun kira taron majalisar zartarwa (NEC) kan wasu muhimman batutuwa
- Daga cikin abin da taron zai maida hankali harda yiwuwar shiga yajin aiki biyo bayan cin mutuncin da aka yi wa shugaban NLC
- Za kuma su tattauna kan alƙawurran da gwamnatin tarayya ta yi a yarjejeniyar MoU da suka sanya wa hannu a watan Oktoba
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC sun kira babban taron majalisar zartarwa wanda suka bayyana da na musamman a Abuja.
Mataimakin shugaban ƙungiyar TUC na ƙasa, Tommy Etim, shi ne ya bayyana haka yayin hira da wakilin jaridar Punch ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, 2023.
Abubuwan da zasu tattauna a zaman
Manufar kiran wannan taron, a cewarsa, ita ce mazari kan yiwuwar tsunduma yajin aikin biyo bayan cin zarafin da aka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a jihar Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bayan haka taron zai tattauna da yin duba kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da ƙungiyoyin kwadago suka rattaɓa wa hannu bayan cimma matsaya da gwamnati ranar 2 ga watan Oktoba.
Ƙungiyoyin kwadagon sun zauna tare da cimma matsaya da gwamnatin tarayya biyo bayan cire tallafin man fetur, wanda ga jefa ƴan Najeriya cikin ƙuncin rayuwa.
Vanguard ta tattaro a kalamansa yana cewa:
"Za mu gudanar da wani babban taron NEC a kowane lokaci daga yanzu. Abin da zamu tattauna sun hada da rashin adalcin da aka yi wa kwamared Ajaero, da kuma yajin aikin da aka shirya."
"Haka nan taron zai yi duba ga yarjejeniyar MoU da muka rattaba hannu da gwamnatin tarayya. Za ku samu cikakkun bayanai bayan mun kammala taron."
Idan baku manta ba, NLC da TUC sun bada wa'adin kwanaki 5 daga ranar Jumu'a kan kama shugaban ƙungiyar kwadago na ƙasa, Joe Ajaero, a Owerri, jihar Imo ranar Laraba.
Ƴan kwadagon sun buƙaci hukumar ƴan sanda ta sauya kwamishinan yan sandan Imo, kana a kama hadiman gwamnatin jihar da suka shirya wannan tuggu.
Gwamnan Abiya ya naɗa Ciyamomi
A wani rahoton kuma Gwamna Alex Otti na jihar Abiya ya naɗa shugabannin da zasunjagoranci kananan hukumomi 17 da ke faɗin jihar.
Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, Prince Uzo Nwachukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa.
Asali: Legit.ng