Manufofin CBN Da Tinubu Sun Fara Aiki, Naira Za Tayi Daraja, Tsohon Sanatan PDP
- Ben Murray Bruce ya yabawa tsare-tsaren da sababbin shugabannin bankin CBN su ka kawo a ‘yan watannin bayan nan
- ‘Dan siyasar ya na da ra’ayin cewa sakin farashin kudin kasar waje a kasuwa shi ne mafita na halin da tattalin arziki ke ciki
- Naira za ta cigaba da yin daraja sannan Sanata Ben Murray Bruce ya yi albishir da cewa ana shigo da hannun jari daga ketare
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ben Murray Bruce ya na cigaba da tofa albarkacin bakinsa a game da halin da Najeriya ta ke ciki a yau bayan yin canjin gwamnati.
‘Dan siyasar ya yi amfani da shafinsa na Twitter kamar yadda ya saba, ya na mai nuna tattalin arzikin Najeriya ya na bunkasa a hankali.
Sanata Ben Murray Bruce ya shaida cewa alkaluma sun nuna tattalin arzikin Najeriya ya fara bunkasa bayan karya darajar Naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ben Bruce: "Tattalin arziki zai mike"
Shawarar da tsohon ‘dan majaliar na Bayelsa ta yamma ya bada shi ne a tabbata tsare-tsaren da ake fitowa da su sun taimaki talakawa.
"Naira ta na kara daraja. Sakin farashi da aka yi a kasuwa ya na aiki. Fitch Ratings sun tabbatar da tattalin arzikinmu ya yi karfi, ya na cigaba.
Gyara-gyaren su na aiki. Tattalin arzikin Najeriya ya koma jawo hannun jari daga waje.
Bankunanmu su na samun riba. Abubuwa su na kyau. Yanzu sai gwamnatin Tinubu ta tabbata nasarorin nan sun kai talakawan Najeriya.
Sannan tsare-tsare kamar karin N35, 000 a albashi da fito da tashoshin CNG sun yi daidai. Akwai dalilin imani cewa abubuwa za su gyaru."
- Ben Murray Bruce
Kafin nan kuma an ji tsohon ‘dan majalisar ya na yabawa Yemi Cardoso saboda tsare-tsaren da ya kawo a matsayin gwamnan bankin CBN.
Bruce yake cewa Dr. Cardoso ya farfado da tattalin arziki a sakamakon manufofin da ya fito da su a bangaren man fetur da kuma canjin kudi.
A ‘yan kwanakin nan, Naira ta daina mummunan faduwar da ta ke yi a kasuwar canji.
Najeriya ta yi asarar man N4.3tr
Labari ya zo cewa hanguna miliyan 208 aka sace ta hanyar fasa bututu, saboda haka ake asarar kudin shigan da ya kai Naira biliyan 2.3 a kullum.
Idan da gangunan man sun shiga kasuwa, da abin da gwamnati zata samu ya zarce Dala miliyan 12 kimanin Naira Tiriliyan 4.325 aka tafka asara.
Asali: Legit.ng