Yan Boko Haram Sun Sake Yi Wa Manoma 9 Yankan Rago a Borno

Yan Boko Haram Sun Sake Yi Wa Manoma 9 Yankan Rago a Borno

  • Mayakan Boko Haram sun sake kashe manoma 13 a wani sabon hari da suka kaddamar a Zabarmari, jihar Borno
  • Wata majiya ta shaida cewa a yayin harin, 'yan ta'addan sun ajiye bindigogin su tare da yin amfani da adduna da wukake wajen yi wa manoman yankan rago
  • Ba wannan ba ne karo na farko da mayakan Boko Haram ke kai hare-hare yankin Zabarmari, sai dai akan yi asarar rayuka da dama a kowanne hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - Akalla manoman shinkafa tara daga yankin Zabarmari ne suka rasa rayukansu a wani hari da Boko Haram ta kai wasu garuruwan Borno, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwan N5.5bn: Abin da ’yan Najeriya suka shuka ake girba – Tsohon dan takarar shugaban kasa

A cewar Zagazola Makama, wata mujallar da ke ruwaito ayyukan ta'addanci a yankin Tafkin Chadi, lamarin ya afku ne a ranar Lahadi yayin da manoman ke girbin amfanin gonarsu.

Sojojin Najeria
Ba wannan ne karo na farko da mayakan Boko Haram ke kai hare-hare a yankin Zabarmari ba Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Zabarmari wani garin manoma ne da ke kilomita 25 daga cikin garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Garin ya shahara a noman shinkafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mujallar ta wallafa cewa 'yan ta'addan sun mamaye garin haye kan mashina masu yawa, inda su ka raba kawunansu gida uku, kafin daga bisani suka far wa manoman.

Yan ta'adda dauke da muggan makamai sun far wa gonakin shinkafa tare da farmakar manonan da ke girbin amfanin gonarsu a kauyukan Koshebe, Karkut da Bulabulin, a karamar hukumar Mafa, kilomita 20 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno."

A cewar Mujallar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Wata majiya ta shaida wa Makama cewa a yayin harin, 'yan ta'addan sun ajiye bindigogin su tare da yin amfani da adduna da wukake wajen yi wa manoman yankan rago.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da walkiya ta kashe dalibai suna tsaka da buga kwalla a Anambra

Majiyar ta ce akalla gawarwakin manoma tara ne aka gano a ranar Lahadi, yayin da da dama suka yi batan dabo, har yanzu ba a gansu ba.

An shafe shekaru ana kai hare-hare a yankin Zabarmari - Rahotanni

Jami'an tsaro da kuma hadin guiwar jami'an sa kai na CJTF a Borno na ci gaba da neman sauran manoman da suka bata.

Tsawon shekaru kenan, manoma a Zabarmari ke fuskantar hare hare daga mayakan Boko Haram, wadanda sau tari ake kashe su ko ayi garkuwa da su yayin hare-haren.

Ko a watan Nuwamba 2020, akalla manoma 45 ne daga garin Zabarmari 'yan ta'adda suka kashe a kauyen Kwashabe, kilomita 20 daga Arewacin Maiduguri.

Mayakan Boko Haram sun dauki alhakin harin Zabarmari

Irin hakan ta taba faruwa a watan Disamba na shekarar 2020, inda kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta dauki alhakin wani hari da aka kai garin Zabarmari na jihar Borno, kamar yadda jaridar Legit Hausa ta ruwaito.

A wani bidiyo da ta saki, kwamandan kungiyar ya yi jawabi na cewa sun aiwatar da kisan kiyashin ne domin rama kisan mambobinsu da sojojin Najeriya suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel