Zabarmari: An sake gano sabbin gawarwaki 35 bayan sun fara kumbura
- An sake gano wasu sabbin gawarwaki 35 a yankin Zabarmari, jihar Borno, a cigaba da neman gawar manoman da aka kashe
- A ranar Asabar ne mugayen 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram suka shiga gonakin kauyen Zabarmari tare da tafka muguwar barna
- Ba tare da girmama rai ko rayuwar dan adam ba, mayakan Boko Haram sun daure manoman, sun yankasu, sannan sun kone gonakinsu
Tawagar hadin gwuiwa ta sojoji da fararen hula (CJTF) sun sake gano karin akalla gawarwaki 35 da suka fara kumbura a yankin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno.
Sabbin gawarwakin 35, wadanda aka gano ranar Litinin, daban su ke da 43 da aka yi jana'izarsu, hakan ya sauya alkaluman mutanen da aka tabbatar an kashe zuwa mutum 78.
An fara tsara neman gawarwakin sauran mutanen a ranar Lahadi amma sai hakan ba ta samu ba.
Jaridar HumAngle ta rawaito cewa tawagar da ta gano gawarwakin ta binnesu nan take saboda ba za'a iya motsa su daga wuraren da suka fara rubewa ba.
KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43
A ranar Lahadi ne gwamnan jihar Borno, Babagana Umar Zulum, ya jagoranci jana'izar gawarwaki 43 na manoman da aka fara samun rahoton cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun yi wa yankan rago.
A ranar Asabar ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan Boko Haram sun shiga ƙauyen Zabarmari, sun bi manoma har gonakinsu tare da hallakasu ta hanyar yi musu yankan rago.
Zabarmari kauye ne mai nisan kilomita 20 kacal daga hedikwatar rundunar atisayen Lafiya Dole wacce ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Majalisar dinkin duniya (UN) ta rawaito cewa a kalla mutane 110 aka kashe, lamarin da ke nuni da cewa an samu karuwar adadin mutanen daga 43 da aka rahotanni suka fara sanarwa.
KARANTA: Korafi: Pantami ya dauki alkawarin isar da sakon 'yan arewa ga Buhari
Ana zargin cewa bayan kisan manoman, mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mata ma su yawa.
"Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a kan fararen hula maza da mata yayin da suke girbe amfanin da suka shuka a gonakinsu," a cewar Edward Kallon, shugaban ayyukan UN na ceto a Najeriya.
."Wannan shine hari mafi girma da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kan fararen hula a cikin shekarar nan. Ina kiran a tabbatar da cewa wadannan miyagu sun shiga hannu domin su fuskanci hukunci," kamar yadda Kallon ya bayyana a cikin jawabin da ya fitar ranar Lahadi.
Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.
A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng