Da dumi dumi: Mayakan Boko Haram sun dauki alhakin harin Zabarmari

Da dumi dumi: Mayakan Boko Haram sun dauki alhakin harin Zabarmari

- Boko Haram ta yi ikirarin cewa ita ta kaddamar da kisan kiyashi a garin Zabarmari, Borno

- A cewar wani kwamandan kungiyar, sun aiwatar da mummunan harin ne domin fansar mutanensu da sojojin Najeriya suka kashe

- Ya kuma gargadi yan farar hula a kan su guji yi musu leken asiri ko su dandana kudarsu

Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta dauki alhakin harin da aka kai garin Zabarmari na jihar Borno.

A wani bidiyo da ta saki a ranar Talata, kwamandan kungiyar ya yi jawabi a faifan inda ya bayyana cewa sun aiwatar da kisan kiyashin ne domin rama kisan mambobinsu da sojojin Najeriya suka yi.

Kungiyar ta gargadi yan farar hula da su guji yin leken asiri a kansu, shafin HumAngle ta wallafa a Twitter.

Da dumi dumi: Mayakan Boko Haram sun dauki alhakin harin Zabarmari
Da dumi dumi: Mayakan Boko Haram sun dauki alhakin harin Zabarmari Hoto: @GovBorno/@HumAngle_.
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hatsaniya ya kaure a majalisa kan bukatar gayyatar Buhari

A ranar Asabar ne kungiyar yan ta’addan ta yiwa wasu manoman shinkafa kisan kiyashi inda ta kashe akalla mutane 43 a jihar ta Borno.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta bukaci Buhari ya sallami Buratai, Sadiqu Baba, dss

A halin yanzu, biyo bayan kisan manoma 43 a jihar Borno wanda yan Boko Haram suka yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sauya tsarin tsaro a Najeriya.

Dr. Ahmad Lawan ya yi kiran ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa domin yi wa gwamnati da mutanen Borno jaje kan mummunan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.

A cewar Lawan, tsarin da ake dashi a kasa baya aiki, inda ya kara da cewa gwamnati na bukatar samun sabbin manufofi da kuma ganin yadda tsarin tsaron zai inganta.

A gefe daya kuma, Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin watsa labarai, ya ce kiraye-kiraye da ake yi na a sallami shugabannin tsaro baya kan layi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng