Jirgin Ruwan N5.5bn: Abin Da ’Yan Najeriya Suka Shuka Ake Girba – Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa
- Yan Najeriya sun fara girbar abin da suka shuka tun yanzu, cewar abokin adawar Tinubu kan jirgin ruwan Naira biliyan 5.5 na shugaban kasa
- Adewole Adebayo, ya ce irin makudan kudaden da 'yan takara ke kashe wa yayin gudanar da yakin zabe alama ce ta cewar almubazzaranci ne a rayuwarsu
- Tsohon dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar SDP ya ce ya zama wajibi 'yan Najeriya su san irin shuwagabannin da za su rinka zaba domin shugabantar su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar SDP a zaben 2023, Yarima Adewole Adebayo, ya ce dole 'yan Najeriya su ci gaba da jure rayuwar almubazzaranci da shuwagabannin da ke mulki yanzu ke yi saboda su suka jawo.
Adebayo ya fadi hakan a martani kan rahotan shirin gwamnati na kasafin kudin 2024, inda za a kashe Naira biliyan 2.6 don kula da motocin fadar shugaban kasa, da kuma Naira biliyan 6.2 kan sayen wasu motocin.
Haka zalika, an ware Naira biliyan biyar domin sayen sabbin motoci ga ofishin uwar gidan shugaban kasa, da kuma Naira biliyan 5.5 na sayen jirgin ruwa na alfarma ga shugaban kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin tattaunawarsa da jaridar Daily Trust a ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba, Adebayo ya ce:
"Na sha fadin cewa kuri'un 'yan Najeriya na da tasiri, kuma duk abin da 'yan kasar suka shuka, sai sun girbe shi. Idan har kuna zabar almubazzarai, to tabbas za ku ga almubazzaranci a kasafin kudi."
Yan Najeriya su san irin shuwagabannin da za su zaba - Adebayo
Dan takarar shugaban kasar ya kara da cewa ko kadan rashin kudi ba shi ne matsalar Najeriya ba, rashin shuwagabanni na-gari ne matsalar, inda ya kara da cewa ya kamata mutane su gane yadda dan takara ya yi kamfe, to haka ne zai shugabance su.
Ya kara da cewa:
"Makudan kudaden da suka kashe yayin gudanar da yakin zaben su bai zama ishara kan cewa ba talaka mai cin abinci sau daya ko biyu a rana ne a gaban su idan suka hau mulki ba?
"Ya zama wajibi mu kasance masu yanke hukuncin irin shuwagabannin da mu ke so su mulke mu, domin wannan wani irin mulki ne wanda bai damu da halin da talakawa ke ciki ba."
Babban Kuskure daya da Buhari da Tinubu ke tafkawa - Prince Adebayo
Ko a karshen watan Agusta, Prince Adewole Adebayo, dan takarar jam’iyyar SDP a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da ya gabata, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana bin tafarkin Muhammadu Buhari, wanda ya gabace shi, ta fuskar ji da tattalin arziki.
Da yake magana kan halin da kasa ke ciki da kuma kokarin Tinubu zuwa yanzu, Adewole ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mummunar manufa.
Asali: Legit.ng