Allah ya yiwa babban Malamin addini, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, rasuwa

Allah ya yiwa babban Malamin addini, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, rasuwa

  • Daya daga cikin manyan Malaman addinin Musulunci a duniya ya rigamu gidan gaskiya
  • Manyan Malamai, daliban ilimi, yan uwa da abokan arziki sun yi alhini da addu'an Allah ya jikan Malamin.
  • Sheikh Al-Luhaydan mamba ne na majalisar malamai a kasar Saudiyya gabanin rasuwarsa

RIYADH — Babban Malamin addinin Musulunci, dan kasar Saudiyya, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, ya rigamu gidan gaskiya bayan doguwar jinyar rashin lafiya.

Iyalan Shehin Malamin suka sanar da mutuwarsa a shafin Tuwita, inda suka bayyana cewa ya yi fama a rashin lafiya sosai.

Sheikh Saleh Al-Luhaidan ya rasu yana mai shekaru 90 a duniya.

An yi masa Sallar Jana'iza da rana a Riyadh, babbar birnin kasar Saudiyya.

Allah ya yiwa babban Malamin addini, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, rasuwa
Allah ya yiwa babban Malamin addini, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, rasuwa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ku yiwa 'yayanku tarbiyya bisa al'adunmu, Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye

Wanene Sheikh Saleh Al-Luhaidan?

An haifi Sheikh Al-Luhaidan a garin Bukayriyah dage yankin Al-Qassim a shekarar 1931.

Ya rike mukamai da dama, wanda ya hada da mamban Majalisin manyan Malamai, mamban kungiyar Musulmai ta duniya kuma tsohon Shugaban majalisar koli ta Shariah

A shekarar 1979, shine wanda yayi khudubar aikin Hajji.

Manyan Malamai, daliban ilimi, yan uwa da abokan arziki sun yi alhini da addu'an Allah ya jikan Malamin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel