Mataimakin Shehu Dahiru Bauchi, Sheikh Umar Sulaiman Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Mataimakin Shehu Dahiru Bauchi, Sheikh Umar Sulaiman Ya Rigamu Gidan Gaskiya

  • Sheikh Umar Sulaiman ya rigamu gidan gaskiya a yau Litinin a gidansa dake Kaduna yana da shekara 76
  • Kafin rasuwarsa, shine mataimakin shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi
  • Dan marigayin, Mustapha Sulaiman, shine ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa, yace ya bar yaya 17 da jikoki da dama

Bauchi - Sheikh Umar Sulaiman, mataimakin shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, ya rigamu gidan gaskiya.

Sheikh Sulaiman ya rasu ne ranar Litinin yana da shekara 76 a duniya bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya.

Sheikh Umar Sulaiman
Mataimakin Shehu Dahiru Bauchi, Sheikh Umar Sulaiman Ya Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ɗan marigayin, Khadi Mustapha Suleman, wanda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa ga wakilin dailytrust, yace a halin yanzu ana shirye shiryen yi masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Shine mataimakin Dahiru Bauchi

A jawabin saanar da mutuwar mahaifinsa, Mustapha yace:

"Mahaifina sheikh Umar Sulaiman ya rasu yau Litinin da yamma a gidansa dake Unguwan Kanawa, jihar Kaduna bayan wata gajeruwar rashin lafiya, yana da shekara 76."

"Har zuwa rasuwarsa, shine mataimakin shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, kuma shugaban al'umma ne sannan malami ne."

Mustapha Sulaiman ya ƙara da cewa marigayi mahaifinsa ya rasu ya bar 'ya'ya 17 da jikoki da dama.

A wani labarin kuma Motar Kwastam Ta Yi Kan Jama'a Ta Hallaka Mutum 5 Yayin Bin Yan Shinkafa a Katsina

Wata motar kwastam ta kucce ta yi kan jama'a yayin da ta biyo yan fasa kwauri a garin Jibia dake jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin da ya afku ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 5 tare da jikkata wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel