Yayin da Ake Shirin Yanke Hukunci a Kano, IPAC Ta Tura Sako Ga Abba Kabir Kan Nade-Naden Mukamai
- Kungiyar IPAC ta shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf kan nade-naden da ya kamata ya yi a gwamnatinsa
- IPAC ta ba da shawarin ne ga gwamna don inganta dimukradiyya inda ta bukaci ya rinka bai wa sauran jam’iyyu mukamai
- Kungiyar ta bayyana haka ne a jiya Lahadi 5 ga watan Nuwamba wanda wakilin shugaban IPAC, Ralph Nwosu ya jagoranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Kungiyar Gamayyar Jam’iyyu, IPAC ta shawarci Gwamna Abba Kabir na jihar Kano kan nade-naden mukamai.
IPAC ta bukaci Abba Kabir da ya rinka nada mukaman gwamnatinsa har zuwa wasu jam’iyyun adawa ba iya NNPP kadai ba.
Mene IPAC ke cewa kan Abba Gida Gida?
Shugaban kungiyar African Democratic Congress, Cif Ralph Nwosu shi ya yi wannan kira a jiya Lahadi 5 ga watan Nuwamba a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nwosu ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a otal din Tahir bayan ziyarar gani da ido na ayyukan gwamnan a jihar, cewar Daily Post.
Ya ce tabbatar da gwamnatin hadaka da babu son kai a ciki zai kara kawo ci gaba a jihar da kuma inganta dimukradiyya.
Wace shawara IPAC ta bai wa Abba Gida Gida?
Ya ce:
“Kada ka mayar da nade-naden gwamnatinka iya ‘yan jam’iyyar NNPP saboda bai wa sauran jam’iyyun adawa zai kawo ci gaba a jihar da inganta dimukradiyya."
Har ila yau, kungiyar wacce ta hada da shugabannin dukkan jam’iyyun Najeriya ta yabawa gwamnan kan ayyukan da ya ke yi a jihar, cewar Tribune.
Ta kuma bayyana irin gudunmawar da ya bayar a bangarori da dama da su ka hada da ilimi da lafiya da harkar noma da sauransu.
Nwosu wanda ya yi magana a madadin shugaban IPAC, Sani Yabagi ya ce makasudin wannan rangadi a kasar shi ne don samar da shugabanci na gari.
A yau kotu za ta yanke hukuncin zaben Kano
A wani labarin, kotun daukaka kara ta sanar da yau Litinin a matsayin ranar yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Kano.
Wannan na zuwa ne bayan kotun zabe ta rusa zaben Abba Kabir tare da tabbatar da Nasiru Gawuna wanda ya lashe zabe.
Asali: Legit.ng