Karya Darajar Naira Ya Jawo Ana Bin Kowane ‘Dan Najeriya Bashin N418, 000 a Yau

Karya Darajar Naira Ya Jawo Ana Bin Kowane ‘Dan Najeriya Bashin N418, 000 a Yau

  • Tasirin karya naira da babban bankin CBN ya yi, ya bayyana wajen bashin da ake bin gwamnatin Najeriya a yanzu
  • A maimakon a ce Najeriya za ta biya bashin naira tiriliyan 57, matakin da aka dauka ya jawo karin naira tiriliyan 20
  • Kafin a je ko ina, sabon shugaban kasa watau Bola Tinubu ya na shirye-shiryen cin bashin kudi daga kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A sakamakon karya darajar Naira, adadin bashin da ake bin gwamnatin Najeriya ya karu da N20.6tr a cikin watanni biyar kacal.

Wani rahoto da aka samu daga Daily Trust ya nuna shirin da gwamnati mai-ci ta ke yi na aro wasu kudi zai iya jawo bashin ya kai N89.2tr.

Kara karanta wannan

Bashin N500bn da Ganduje ya bari ne ya hana mu fara aiki kan lokaci, Gwamnatin Kano

Bashi
Ana bin Najeriya bashin N87tr a mulkin Bola Tinubu Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Tinubu zai fara da cin bashin kudi

Idan Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarar cin sabon bashi, zai zama zuwa Disamba ana bin duk mutumin Najeriya bashin da ya kai N418,779.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Yunin bana, bayan Bola Tinubu ya karbi mulki daga hannun Muhammadu Buhari, bashin da ake bin kasar $113.4b (N87.4tr) ne.

Bankin CBN ya karya Naira

Bankin CBN ya na lissafin $1 a kan N770.38, hakan zai nuna nauyin bashin a kudin Najeriya bayan an karya Naira daga N460 a kan Dala.

Bayanan da aka samu daga ofishin kula da bashi na DMO, ya nuna bashin da ke wuyan kasar a 2005 (wanda da aka yafe) $18bn ne.

Ministan kula da tattalin arziki da kudi, Wale Edun ya fada wajen taron IMF cewa gwamnati za ta karbo aron $1.5bn daga bankin Duniya.

Kara karanta wannan

Hobbasan sabon Gwamnan bankin CBN ya yi sanadiyyar zaburar darajar Naira

An yarda a karbo bashin $7.8bn da €100m

Bayan haka akwai bashin $7.8bn da €100m da sabon shugaban kasar ya nema, kuma majalisar dattawa ta amince da bukatar da aka gabatar.

Da an cigaba da canza Dala a kan N460, jaridar ta ce bashin da ake bin Najeriya ba zai wuce N57.6tr, karya Naira ya jawo bashin ya karu sosai.

Bayan zuwan Tinubu ne bankin CBN ya karya Naira da N315 a kan Dalar Amurka, kwatsam hakan ya jawowa Najeriya karin bashin N20.6tr.

Tsare-tsaren da Tinubu ya zo da su

Watanni biyu da zama Shugaban Najeriya, sai aka ji cewa Bola Ahmed Tinubu yana fuskantar fushin al'umma saboda masifar tsadar rayuwa.

Soke tsarin tallafin man fetur da karya darajar Naira na cikin tsare-tsaren da ake kuka ta da su wanda masana su ka ce hakan na da hadari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng