Ba Barawo Ba ne: Abin da Ya sa Ake Cewa Janar Abacha Ya Saci Kudi Inji Jigon PDP

Ba Barawo Ba ne: Abin da Ya sa Ake Cewa Janar Abacha Ya Saci Kudi Inji Jigon PDP

  • Uche Rochas bai cikin wadanda su ka yarda da abin da ake fada a game da Marigayi Janar Sani Abacha
  • ‘Dan siyasar ya wanke tsohon shugaban Najeriyan, ya ce babu wata satar da ya yi a lokacin da ya ke kan mulki
  • A cewar Arch. Rochas, dukiyar da ake ikirarin Marigayi Abacha ya sata, kudin man da Najeriya ta saida ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Uche Rochas ya na cikin jagororin jam’iyyar PDP a Najeriya, ya fito ya yi magana da ta zama kariya ga Marigayi Sani Abacha.

A lokacin da ake zargin tsohon shugaban Najeriyan da satar baitul-mali, Arch. Uche Rochas ya fayyace yadda abin yake a shafin Twitter.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Yayin da yake magana a shafinsa, ‘dan siyasar ya musanya zargin da ake jifan Janar Sani Abacha da shi na satar dukiyar kasa a kan mulki.

Sani Abacha
Janar Sani Abacha Hoto: www.bbc.com, www.reuters.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Sani Abacha ya saci kudi?

Rochas ya ce yadda mutane su ke tunani ba haka abin yake ba, Janar Abacha ba barawo ba ne, wannan magana ta tada kura a dandalin.

"Janar Sani Abacha bai saci wani kudin Najeriya daga baitul-mali ba, ya saida man mu ne ta hannun wasu saboda takunkumi.
"Bayan mutuwarsa, su na so su karkatar da kudin amma sai ‘yan fallasa su ka tona asiri, sai yanzu su ke cewa dukiyar ta zama sata."

- Uche Rochas

An yi wa Rochas raddi a kan Sani Abacha

Nan take wasu su ka maida masa martani cewa shakka babu tsohon shugaban ya yi sukuwa a kan baitul-mali da ya ke karagar mulki.

Kara karanta wannan

“Ni ba waliyyi bane, Najeriya ba ta da matsala”, In ji Peter Obi

Masu bibiyar al’umuran yau da kullum irinsu H. A Hayatu sun goyi bayan maganar, ya ce dalolin da ake dawowa da su ba na sata ba.

Takunkumin da aka daurawa Gwamnatin Abacha

"An kakabawa Najeriya takunkumi a zamanin Abacha amma gwamnati ta cigaba da dawainiyarta na biyan albashi da kwangiloli.
“Kun san ta ya? Ta hanyar saida mai ta hannun wasu a bayan fage, lokacin da ya mutu sai su ka kira kudin da dukiyar sata.
Shiyasa yanzu ake cewa an dawo da kudin sata. Kudin man da Najeriya ta saida ne.”

H. A Hayatu

Za a dawo da $150m da Abacha ya 'sace'

Abin da ya jawo wannan shi ne an samu labari gwamnatin Faransa ta yi alkawarin maido dala miliyan 150 da ta ce an sace a zamanin Abacha.

An ji haka ne a lokacin da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tarbi jakadan Shugaba Emmanuel Macron a fadar Aso villa da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng