Ana Zargin Basaraken Jigawa da Lalata Yarinya Tare da Sa Mata Cutar Kanjamau

Ana Zargin Basaraken Jigawa da Lalata Yarinya Tare da Sa Mata Cutar Kanjamau

  • An zargi wani hakimin kauyen Jigawa, Umar Ibrahim, da yiwa yarinya fyade da ciki sannan ya shafa mata cutar kanjamau
  • Sai dai kuma, Ibrahim ya karyata zargin yana mai cewa iyayen yarinyar na kokarin bata masa suna ne
  • Binciken sashen binciken manyan laifuka na rudunar yan sandan jihar ya zargi Umar Ibrahim da kitsa aikata barna da aiwatar da fyade.

Jihar Jigawa - Wani mutum mai suna Ya'u Muhammad, ya zargi hakimin kauyen Dan Gulam da ke karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, Umar Ibrahim, da yiwa diyarsa fyade, tare da kunsa mata ciki sannan ya sa mata cutar kanjamau.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, an yi zargin ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 16 ga watan Oktoba 2023 da taken "Sanarwar gurfanar da Umar Ibrahim (Hakimin kauyen DanGulum) kan laifin fyade wanda ya yi karo da sashi 3 (1) (A da D) na dokar VAPP 2021".

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar a runtuma kame, 'yan kauye sun yi wa alkali jina-jina a jihar Gombe

Taswirar jihar Jigawa
“Bata Mun Suna Suke Kokarin Yi”: An Zargi Basaraken Jigawa da Lalata Yarinya, Ya Shafa Mata Kanjamau Hoto: Map of Jigawa state
Asali: Facebook

Wasikar ta ce:

"Atoni Janar na jihar Jigawa ya umurceni da na rubuto wasika sannan na sanar da mai martaba cewa, wani Ya'u Muhammad ya kai korafin fyade inda ya yi zargin cewa Umar Ibrahim (hakimin kauyen Dan Gulam) ya yi wa diyarsa fyade wanda ya yi sanadiyar da ta dauki ciki sannan ya sa mata cutar Kanjamau."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kokarin bata mun suna ne, basaraken Jigawa

Sai dai kuma, hakimin kauyen ya ce ba shine ya yi wa yarinyar ciki ba.

"Suna kokarin bata mani suna ne. Wannan ne dalilin da yasa suka yi mani kage cewa na yi mata ciki. Ban san yarinyar bane, ban taba haduwa da ita ba ko sau daya a rayuwata.
"Ina da cutar Kanjamau tsawon sama da shekaru 10 lokacin da na auri wata bazawara da ke dauke da cutar. Wannan ne dalilin da yasa suka ce na shafawa yarinyar, amma na rantse ban aikata ba."

Kara karanta wannan

So gamon jini: Daga yanke mata farce, kyakkyawar budurwa ta fada soyayya da mai yankan kumba

Basaraken ya maka yarinyar, mahaifinta da wani Sule Umar na kauyen Dangulam a gaban kotun Shari'a da ke Gwaram, Trust Radio ta rahoto.

An rahoto cewa binciken sashen binciken manyan laifuka na rudunar yan sandan jihar ya zargi Umar Ibrahim da kitsa aikata barna da aiwatar da fyade.

Matar aure ta koka bayan duba wayar mijinta

A wani labarin, mun ji cewa wata yar Najeriya ta duba wayar mijinta sannan ta karaya da sakon da ya aikewa daya daga cikin abokan aikinsa a WhatsApp.

Matar auren da ba a bayyana sunanta ba ta yada sakon a dandalin Facebook, yayin da take neman shawara kan abun yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng