Rikicin Makiyaya da Manoma: Makiyaya Sun Sare Hannun Wani Manomi a Yayin Rikici

Rikicin Makiyaya da Manoma: Makiyaya Sun Sare Hannun Wani Manomi a Yayin Rikici

  • Rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya, an sare wa manomin shinkafa hannu a rikicin
  • Rahotanni sun ce makiyayan sun shiga gonar mutumin ne tare da tura shanunsu su cinye komai
  • An kai rahoton ga hukumar tsaro ta NSCDC dake jihar Kwara, ana kuma kan bincike kan lamarin

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yanke hannun dama na wani manomin shinkafa mai suna Saheed Zakariyau, a kauyen Bindofu dake masarautar Lafiagi, a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, Punch ta ruwaito.

Manomin, a cewar majiyoyi, ana zargin an kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Bindofu a ranar Asabar da ta gabata bayan ya zargi makiyayan da ingiza dabbobinsu wajen lalata gonarsa.

An tattaro cewa wanda manomin, tare da abokan aikinsa, ya je gonar a ranar Asabar kuma ya gano cewa makiyayan sun yi kiwon shanunsu a gonarsa tare da lalata amfanin gonar.

KU KARANTA: Bayan Shafe Shekaru 12 Yana Mulki, Firaministan Israi’la Ya Rasa Ikonsa

Makiyaya sun kai hari kan manoma hari, sun yanke hannun wani manomi
Gona da manoma na aiki a cikinta | Hoto: munkgc.com
Asali: UGC

Rahoton da Legit ta samo ya bayyana cewa manomin da abokansa sun fatattaki makiyayan.

Sai dai, an ce daya daga cikin makiyayan ya zaro adda ya datse hannun manomin nan take.

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Demokradiyya da misalin karfe 1 na rana.

Ya ce, “Wani Mista Saheed Zakariyau, tare da abokan aikinsa na yankin Bindofu, Lafiagi, sun zo ofishin NSCDC, reshen Lafiagi, suka ce sun je gonarsu da misalin karfe 9:30 na safe.

"Suna zuwa wurin, sai suka tarar da garken shanu da kuma wasu Fulani makiyaya suna kiwo a gonarsu ta shinkafa.

"A yayin da suke kokarin bin Fulani makiyayan da shanunsu, wani Bafulatani ya ciro adda ya yanke masa hannun dama kuma Bafulatanin ya gudu."

Afolabi ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin tare da cafke wadanda ake zargin.

KU KARANTA: Manya Na Ku Daban: Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin, An harbi wani soja da ke aiki a Birged ta 14 na Sojojin Najeriya a Ohafia a ranar Asabar yayin artabu tsakanin sojoji da wasu ‘yan ta'adda da ake zargin mambobin kungiyar tsaro ta Gabas ce ta ESN, Punch ta ruwaito.

An gano cewa rikicin ya fara ne lokacin da ‘yan ta'addan suka kai hari sanannen tashan mota na Ebem a karamar hukumar Ohafia da ke jihar suka yi ta harbi ba ji ba gani.

Harbe-harben ya sa sojoji suka kawo dauki daga Hedikwatar Soja, a Ohafia, wadanda suka yi musayar wuta da mambobin kungiyar ta ESN.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel