Wani Dan Najeriya Ya Gano Yaransa 4 Ba Nashi Bane Bayan Gwajin DNA, Ya Koka a Bidiyo Mai Tsuma Rai
- Wani dan Najeriya ya bayyana yadda ya gano cewa dukka yaransa hudu ba shine ubansu ba
- Mutumin ya magantu kan yadda sabani tsakaninsa da matarsa ya haddasa masa yi wa yaransa gwajin kwayoyin halitta (DNA)
- Labarinsa mai tsuma zuciya da aka bayar a harshen yarbanci ya haddasa cece-kuce tsakanin masu amfani da soshiyal midiya wadanda suka bayyana muhimmancin gwajin DNA
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani dan Najeriya mai suna, Olarenwaju Kolawole, ya bayyana cewa yara hudu da matarsa ta haifa masa duk ba nasa bane.
Kolawole ya ba da labarinsa a tashar Kokoro Alate, wani shirin gidan radiyo na Yarbanci, yana mai cewa ya gano hakan ne bayan ya yi masu gwajin DNA.
Da yake magana a harshen Yarbanci, mutumin ya ce ya auri matarsa tun a 2007 sannan ya bayyana yadda sabani tsakaninsu yasa shi tunanin yi wa yaransa gwajin kwayoyin halitta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na auri matata tun a 2007, ta haifi yara hudu, gwajin DNA ya nuna cewa babu nawa ko daya a ciki," cewar mutumin.
Bidiyon da shafin @BolanleCole ya wallafa a shafin X ya haddasa muhawara a dandalin.
Kalli bidiyon a kasa:
Bidiyon ya haddasa cece-kuce
@evedenzmusicya ce:
"Babu shaidan....Mutane ne shaidanin."
@Sir_neji ya ce:
"Zama da yara hudu da ganowa cewa yaran ba naka bane bayan shekaru 16, wannan matar shaidaniya ce a cikin mutum."
@Dreamkay15 ta ce:
"Ina ganin lokaci ya yi da ya kamata a duba tsarin DNA. Hauhawan iyaye maza da basu ne ainahin uban 'ya'ya ya fara ba da tsoro."
Ma'aurata sun baje kudin da suka samu
A wani labari na daban, mun ji cewa wasu sabbin ma'aurata sun garzaya dandalin soshiyal midiya don baje kolin makudan kudaden da suka samu a wajen bikin aurensu.
"Don Allah ina so na sake bikin aure," taken da aka yi wa bidiyon da ke nuna ma'auratan da ke kirga kudaden kenan.
A cikin bidiyon, ma'auratan sun jeru a kan katafaren gadonsu yayin da suke tattara kudaden da yin su bandir bandir.
Asali: Legit.ng