'Ku Nemi Ilimin Addinin Kirista, Sarkin Musulmi Ya Magantu Kan Dawo da Zaman Lafiya

'Ku Nemi Ilimin Addinin Kirista, Sarkin Musulmi Ya Magantu Kan Dawo da Zaman Lafiya

  • Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya shawarci dukkan Musulmai kan neman ilimin addini don dakile yaduwar karerayi
  • Sultan ya bayyana haka ne yayin lakcar makon Usman Dan Fadio karo na 10 da aka gabatar a Ilorin babban birnin jihar Kwara
  • Sarkin Musulmi a shawarci Musulman da su dage da neman ilimin addinai daban-daban saboda kawo zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara– Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya shawarci Musulmi da su nemi ilimin addinai da ba na su ba don samun zaman lafiya.

Sultan ya kuma shawarci Musulmai da su nemi ilimin sanin Ubangiji don yin amfani da shi wurin zama mutane nagari, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Sarkin Musulmi ya shawarci al'umma kan neman ilimin addinai
Sultan Sa'ad Abubakar ya shawarci Musulmi kan neman ilimi. Hoto: NSCIA.
Asali: UGC

Mene Sarkin Musulmi ke cewa?

Sarkin Musulman ya bayyana haka ne a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba a Ilorin babban birnin jihar Kwara yayin lakcaR Usman Dan Fodio karo na 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kirkiri taron ne don martaba makon Usman Dan Fodio da aka fara a jihar Sokoto.

Ya ce makasudin wannan lakca ta shekara an kirkire ta ne don kara wa Musulmai kwarin gwiwar neman ilimin addini da kuma amfani da shi.

Wane shawara ya bai wa Musulmi?

Ya ce:

“An kafa masarautar Sokoto ce kan turbar neman ilimi ba rashinsa ba, saboda haka ya zama wajibi ga Musulmai su nemi ilimi kuma su yada zuwa ga ‘ya’yansu.
“Hakan shi zai rage yawan jita-jita da karairayi idan har an nemi ilimin da ya dace na addini.”

Sultan ya ce sun zabi Ilorin ne don nuna wa duniya cewa Musulunci abu daya ne kuma ba tare da bambanci ba, Royal News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko ta bankaɗo wasu illoli da ƴan bindiga suka yi a Jihar Katsina

Ya kara da cewa:

“Meyasa mu ka zabi Ilorin, wasu za su iya tambaya saboda akwai matsaloli na cewa mu kai shi Legas ne ko sauran birane.
“Mun zo nan ne don ilmantar da ‘yan uwanmu don sanin irin sadaukarwa da kakanninmu su ka yi don dabbaka Musulunci.”

Yayin gabatar da lakcan, Sheikh Zakir Naik ya yi jawabi kan sanin ubangiji a manyan addinan duniya.

Sultan ya yi martani kan ma su cece-kuce ga Zakir Naik

Kun ji cewa, Sarkin Musulmai, Sa'ad Abubakar ya yi martani kan ma su cece-kuce kan gayyatar Sheikh Zakir Naik zuwa Najeriya.

Sultan ya ce a matsayinsu na Musulmai su na da damar gayyatar kowa don fadakar da mutane addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.