Zaben Bayelsa: Gwamna Diri Na Bayelsa Ya Shiga Matsala Ana Dab da Zabe

Zaben Bayelsa: Gwamna Diri Na Bayelsa Ya Shiga Matsala Ana Dab da Zabe

  • Ana gab da a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa, an buƙaci kotu ta soke takarar Gwamna Diri da mataimakinsa
  • Wata mata ce dai ta shigar da ƙara a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ra nemi a hana mataimakin gwamnan yin takara saboda rashin cancantarsa
  • Mai shigar da ƙarar ta nemi kotun da ta bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da ƴan takara a zaɓen gwamnan na ranar 11 ga watan Nuwamba

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙasa da kwanaki a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa, an shigar da wata sabuwar ƙara ta neman soke takarar gwamna Douye Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo, a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu ta kwace kujerar sanatan PDP, ta tabbatar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zabe

Ƙarar dai ta nemi umarnin tilasta hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta cire sunayen Diri da Ewhrudjakpo a matsayin ƴan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Premium Times.

An nemi kotu hana Gwamna Diri yin takara
An bukaci kotu ta hana Gwamna Diri takara a zaben Bayelsa Hoto: Duoye Diri
Asali: Facebook

Haka kuma ta nemi a ba da umarnin dakatar da INEC, da wakilanta daga cigaba da buga sunayen su a matsayin masu ƴan takarar jam'iyyar a zaɓen gwamnan na jihar Bayelsa, rahoton The Nation ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka shigar ƙarar kan Diri da mataimakinsa?

Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1448/23, wacce wata mata daga Bayelsa, Blessing Azibanagbal, ta shigar da ita ta hannun lauyanta, Ifeanyi Nsowu, ta ƙara neman a bayyana cewa Mista Ewhrudjakpo bai cancanci tsayawa takarar mataimakin gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar PDP ba.

Azibanagbal, a cikin ƙarar da ta shigar a ranar 30 ga Oktoba, ta nemi a bayyana cewa Mista Ewhrudjakpo bai cancanci zama abokin takarar Gwamna Diri ba.

Kara karanta wannan

"Ina da bidiyo" Sanata ta tona asirin gwamnan arewa, ta faɗi yadda ya yi yunƙurin kashe ta

Ta roƙi kotun da ta bayyana cewa Mista Ewhrudjakpo yana da sunaye da yawa ba tare da wata shaida da ta tabbatar da "mutum ɗaya ne ba."

Domin haka ta buƙaci kotun da ta bayyana cewa PDP ba ta da ɗan takara a zaɓen.

Ƙarar ta kuma nemi a bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da wani ɗan takara da ya cancanta tsayawa takarar gwamna a Bayelsa.

Gwamna Diri, Mista Ewhrudjakpo, PDP da INEC sune waɗanda ake ƙara na ɗaya zuwa na huɗu a kan lamarin.

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Takarar Sylva

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta zartar da hukunci kan matsayin takarar Timipre Sylva na APC a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.

Kotun ta warware hukuncin da wata kotu ta yi na hana Sylva yin takara a zaɓen gwamnan na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng