‘Ba Alkalai Suka Janyo Min Rashin Nasara a Kotu Ba’, Tsohon Gwamnan PDP, Suswam

‘Ba Alkalai Suka Janyo Min Rashin Nasara a Kotu Ba’, Tsohon Gwamnan PDP, Suswam

  • Gabriel Suswam, ya ce ba zai dora laifin faduwarsa zabe akan alkalan kotun daukaka kara ba, sai dai yana jin tsoron makomar fannin shari'ar kasar
  • A cewar Suswan, dokar da alkalin wata kotu yayi amfani da ita wajen yanke hukunci, ya kamata wani alkalin ma ya yi amfani da ita wajen kafa hujja
  • A baya bayan nan ne kotun daukaka kara ta kwace kujerarsa ta sanata mai wakiltar mazabar Benue ta Arewa maso Gabas, tare da mikata ga dan takarar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam wanda a bayan nan kotu ta kwace kujerarsa ta sanata mai wakiltar mazabar Benue ta Arewa maso Gabas, ya ce bai zargi alkalan kotun daukaka kara da suka yanke hukuncin shari'arsa da zama silar rasa kujerar sanata ba.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan sahihancin zaben dan majalisar Tarayya a NNPP, Jibrin

A ranar Laraba ne kotun daukaka kara a Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron shari'ar zabe da ya nuna cewar Suwam shi ne wanda ya lashe zaben sanatan Benue ta Arewa maso Gabas.

Gabriel Suswam
Tsohon Gwamna Gabriel Suswam, ya ce akwai matsala a cikin fannin shari'ar Najeriya Hoto: Gabriel Suswam
Asali: Twitter

Kotun daukaka karar ta kalubalanci hukuncin da kotun sauraron shari'ar zaben 'yan majalisun tarayya na jihar Benue, wacce ta yi watsi da nasarar Emmanuel Udende na jam'iyyar APC, tare da ba Suswam na jam'iyyar PDP takardar shaidar cin zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, kotun daukaka karar ta kuma yi watsi da hukuncin kotun zaben, bisa la'akari da samun kwakkwarar hujja da dan takarar jam'iyyar APC ya gabatar gabanta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Abin da Gabriel Suswam ya ce game da hukuncin kotun daukaka kara

Da ya ke martani kan wannan sabon hukuncin da aka sanar a gidan talabijin na Arise TV, Suswam ya ce:

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan sahihancin zaben dan tsohon minista a jihar Neja

Ina ga babban joji na kasa na da aiki a gabansa na tattara kan dukkanin alkalan kasar, su zauna su duba sabbin dokoki da majalisar tarayya ta gabatar wa shugaban kasa. Ba wai dokar zabe kadai ba, akwai dokoki da dama da majalisar ta gabatar wadanda alkalan za su rinka gani ko ji idan wani lauya ya je gabansu.
Akwai abubuwa da yawa a kasar nan da ya kamata ace mun duba su, ba wai don mun fadi zabe a kotu mu zo muna dora laifin akan alkalai ba.

Ba laifin alkalai ba ne, laifin tsarin shari'ar kasar ne - Suswam

Suswam ya kuma nuna damuwarsa kan yadda kotun sauraron kararrakin zabe ta bashi nasara amma kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin, a cewarsa:

Idan har aka ci gaba da hakan, to mutane za su ci gaba da cire tsammani akan bangaren shari'a na kasar nan. Ya kamata ace, dokar da alkalin wata kotu yayi amfani da ita wajen yanke hukunci, to wani alkalin ma ya yi amfani da ita wajen kafa hujja, idan kuwa ba haka ba, to akwai kalubale da fannin shari'ar zai iya fuskanta nan gaba.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Amma ba zan dora laifin faduwa zabe na ga alkalan da suka yanke hukuncin ba, la'akari da irin muhallin da suke yin aiki a ciki, ba zamu tsammaci wani abin azo a gani daga wajen alkalan ba, har sai an bunkasa muhalli da yanayin aikin na su.

A karshe Suswam ya ce yana ganin laifin tsarin shari'ar ne baki daya ba wai alkalai ba, a cewarsa "lallai akwai matsala tattare da wannan tsarin da fannin shari'a ke tafiya a kansa," a cewar wani rahoto na jaridar Vanguard.

Kotu ta kwace kujerar Sanatan PDP, Gabriel Suwam

A ranar 1 ga watan Nuwamba ne Legit Hausa ta ruwaito maku yadda kotun daukaka kara ta kwace kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas daga hannun Gabriel Suswam, na jam'iyyar PDP, inda ta mika ta a hannun dan takarar jam'iyyar APC.

A wani hukunci da kotun ta yanke, ta ce Gabriel Suswam ba shi ne ainihin wanda ya lashe zaben na ranar 25, ga watan Fabrairu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.