Giwaye Daga Kamaru Suna Shigowa Gonaki a Borno Suna Barna, Majalisa Ta Mika Kuka Ga Tinubu

Giwaye Daga Kamaru Suna Shigowa Gonaki a Borno Suna Barna, Majalisa Ta Mika Kuka Ga Tinubu

  • Giwaye daga kasar Kamaru na ci gaba da zama barazana ga manoma a Borno, lamarin da ya sa majalisar dokokin tarayya ta mika kuka ga shugaba Tinubu
  • Yar majalisa mai wakiltar mazabar Bama/Ngala/Kala Balge a majalisar tarayya, Zainab Gimba ta mika kukan, inda ta ce giwayen na lalata amfanin gonaki
  • Kusan kowacce shekara sai giwaye daga gidan adana namun daji na Waza da ke kasar Kamaru sun shiga jihar Borno ta garuruwan Ngala da Kala Balge

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - Majalisar dokokin tarayya ta yi kira ga Ma'aikatar Muhalli da Kula da Namun Daji ta Kasa, da ta samar da hanyar magance matsalar shigowar giwaye cikin gonakin manoma kowacce shekara, a wasu yankuna na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Ta Maka Wani Mutum a Kotu Kan Bata Mata Suna

Yar majalisa mai wakiltar mazabar Bama/Ngala/Kala Balge a majalisar tarayya, Zainab Gimba (APC, Borno), ta gabatar da wannan kiran, biyo bayan wani kudirin doka na al'amuran da suka shafi jama'a da ke bukatar a duba su cikin gaggawa da majalisar ta tabbatar, a zaman ta na ranar Alhamis.

Majalisa ta koka kan shigowar giwaye gonakin Borno
Majalisar ta mika kuka ga Tinubu inda ta bukaci a kawo karshen shigowar giwayen Borno Hoto: Sa'id Ndanusa
Asali: Twitter

Zainab ta ce giwayen na shigowa ne daga gidan adana namun daji na Waza da ke Kamaru, kuma suna shigowa kowacce shekara, inda suke bi ta kananan hukumomin Ngala da Kala Balge, da ke jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zainab ta ce:

A yayin da suke yawo a cikin gonakin, suna lalata amfanin gona, wanda hakan ke jefa manoma da al'ummar yankunan shiga cikin mawuyacin hali.
"Lalata amfanin gonar na iya kawo cikas ga duk wani shiri da gwamnati take yi na wadatar da abinci a kasa, musamman idan aka yi la'akari da cewa wadannan yankunan na karkashin jami'an soji."

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Zainab na ci gaba da cewa:

"Akwai bukatar samar da kayan aiki da za su iya korar giwayen daga garuruwan, wanda hakan zai kawo karshen lalata amfanin gonakin da kuma sauran abubuwan da suke lalatawa".

An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno

Ko a cikin watan Disambar shekarar 2019, A kalla giwaye 250 kungiyar jin kai ta majalisar dinkin duniya ta hango a Borno, kusa da iyakokin kasashen Kamaru da Chadi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana.

An ga giwayen na tafiya ne zuwa dajin Rann dake karamar hukumar Kalabalge dake jihar Borno, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Yadda giwa ta halaka wata mata, ta bi ta wurin jana'izarta ta tattake gawar

Wani abun mamaki ya faru a kauyen Raipal dake Indiya inda wata katuwar giwa ta halaka wata tsohuwa mai shekaru 70 kuma ta je har inda ake jana'izar tsohuwar tare da tattake gawar.

Kara karanta wannan

An warware rawanin Sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin bisa zargin ya raina Sarkin Yarbawa Olubadan

Giwar ta arce bayan da ta halaka matar yayin da take tara ruwa a kauyen Raipal, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

An garzaya da tsohuwar asibiti inda tace ga garinku sakamakon miyagun raunikan da ta ji, Aminiya ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.