An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

- A kalla gungun giwaye 250 ne wata kungiyar jin kai ta majalisar dinki duniya ta hango a filin dagar Boko Haram

- Kamar yadda rahoton ya bayyana, wannan ne karo na farko da aka ga giwaye a yankin tun bayan fara rikicin Boko Haram

- Kwamishinan muhalli na jihar Borno, ya bayyana cewa wannan alama ce da ke nuni da cewa salama da zaman lafiya ya fara samuwa

A kalla giwaye 250 kungiyar jin kai ta majalisar dinkin duniya ta hango a Borno, kusa da iyakokin kasashen Kamaru da Chadi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana.

An ga giwayen na tafiya ne zuwa dajin Rann dake karamar hukumar Kalabalge dake jihar Borno.

Kamar yadda rahoton RFI ya bayyana, wannan ne karo na farko da aka fara hango giwaye a yankin tun bayan fara rikicin mayakan Boko Haram a yankin.

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya yabawa Buhari kan nasarorin da ya samu a zabe, tattalin arziki da tsaro

Rahoton ya kara da cewa, “Daruruwan giwaye ne ake amfani dasu wajen shige da fice a yankin har zuwa kusan shekaru 10 da suka gabata, bayan fara kai harin mayakan don kafa kasar musulunci.”

“A 2014 ne bangaren Abubakar Shekau na Boko Haram suka kafa sansaninsu a dajin Sambisa. A yayin tsokaci a kan wannan cigaban, Kabiru Wanori, kwamishinan muhalli na jihar Borno din ya sanar da RFI cewa, “wannan nuni ne da cewa zaman lafiya da salama na dawowa yankin.” rahoton ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel