Hobbasan Gwamnan Bankin CBN ya yi Sanadiyyar Zaburar Darajar Naira a Kasuwa
- Dala ta na karyewa a kasuwar canji bayan babban bankin Najeriya ya fara sallamar bankuna bashin kudin waje da su ke bi
- Sabon Gwamnan bankin CBN ya nemo Dalolin da ya fara biyan bankuna, hakan zai taimaka a samu kudin ketaren da su ke wahala
- Duk da Dala ba ta sauka war-was ba, amma ‘yan kasuwa sun ce Naira ta na ta yin daraja musamman a cikin karshen makon nan
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karkashin Babban bankin CBN na kasa, ta fara biyan bashin kudin kasar waje da ake bin ta.
Legit ta samu wannan labari ta majiyoyi dabam-dabam, an fara biyan kudin ne a jiya.
Bankuna sun fara karbar Daloli
Rahoton Punch ya nuna ana tunanin akwai bankuna uku: Citi Bank, Stanbic IBTC da Standard Chartered Bank da aka biya duka bashinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ba za a rasa bankunan da har yanzu su ke fama da karancin kudin kasar wajen ba domin CBN bai kai ga biyan bashinsu ba tukuna.
Kamar yadda Ministan tattalin arziki ya bayyana, bashin da bankuna su ke bi ya kai $6.7bn.
Dala 1 ta karye zuwa N1, 120
Labarin biyan bashin bai gama karada ko ina ba sai aka ji cewa darajar Naira ta karu a kasuwar canji, an koma saida Dala daya a kan N1, 120.
Darajar kudin Najeriyan ya karu da N50 ko 4.27% idan aka kamanta da N1, 170 da ‘yan kasuwar canji su ka saida Dala guda a ranar Larabar nan.
Menene tasirin abin da CBN ya yi?
Masu harka da kudin kasashen waje sun ce wannan mataki da CBN ya dauka zai taimaka wajen samar da kudi da farfado da kasuwar canji.
Shugaban kungiyar ACTN, Adeyinka Ogunnubi, ya fitar da jawabi inda ya yabawa bankin CBN, ya ce za su cigaba da goyon bayan irin hakan.
Shi ma Wale Oyerinde ya ce sabon Gwamnan da aka nada ya nuna da gaske yake yi duk da babu isasshen dalolin da za a dauke duka bashin.
‘Yan kasuwa sun ce babban bankin ya yi abin a-yaba, sai dai ana tsoron bankunan kasuwa za su iya fusata lamarin, su kawowa shirin cikas.
Ana zargin akwai wasu da su ke cin moriyar kafar I & E da aka kirkiro domin masu shigo da kaya daga ketare, su ne ke jawo Dala ta na tashi.
Ana samun saukin Dala a yau
Kwanan nan wani rahoto ya nuna cewa za a samu saukin farashin kayan kasashen ketare saboda faduwar Dala bayan tashin da ta yi a baya.
‘Yan kasuwar canji sun nuna abubuwa sun canza, Dala ta na dawowa kasuwa sannu a hankali, yanzu su na ganin Dalar Amurka ta na yawo.
Asali: Legit.ng