‘So Ake a Kore Mu’, Dilallan Shanu a Abia Sun Musanta Ikirarin Gano Gawarwaki a Kasuwarsu
- Hausawa ‘yan kasuwar shanu da ke Lokpanta a karamar hukumar Umunneochi a jihar Abia sun koka da irin sharrin da aka mu su
- Kakakin ‘yan kasuwar a jihar, Buba Abdullahi shi ya yi wannan zargi inda ya ce wannan shiri ne kawai na korarsu a jihar gaba daya
- Idan ba a mantaba, Gwamna Alex Otti ya ce sun samu gawarwarkin mutane 70 a kasuwar inda ya ce su na ajiye ma su laifuka
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia – Al’ummar Hausawa da ke siyar da shanu a kasuwar Lokpanta a jihar Abia sun koka kan shirin korarsu a kasuwar.
‘Yan kasuwar sun bayyana cewa zargin samun gawarwakin mutane 70 babu kayuna da wata makarkashiya don korarsu a kasuwar, cewar Tribune.
Mene Otti ke zargin Hausawan a kasuwar Lokpanta?
Yayin ganawa da manema labarai, Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ce an samu gawarwaki 70 ba tare da kayuka ba, da kuma kasusuwan mutane a kasuwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kara da cewa binciken sirri ya tabbatar da cewa mafi yawan kudaden fansa na masu garkuwa kasuwar ake kawo wa.
Dalilin haka Otti ya ce ba za su janye dokar ba ta tilasta ‘yan kasuwar barin gidajensu a cikin kasuwar don komawa cikin jama’a makwabta.
Wane martani Hausawan su ka yi kan kasuwar ta Lokpanta?
Yayin da ya ke martani, kakakin Hausawar yankin, Buba Abdullahi ya ki amince wa da wannan matsaya ta Gwamna Otti.
Buba ya musanta zargin gwamnan cewa kasuwar na ajiye ma su laifuka da kuma samun gawarwaki a kasuwar, Daily Trust ta tattaro.
Ya ce akalla su na da yawan mutane dubu 15 inda su ka mamaye fadin kadada 80 na yankin wanda gwamnatin Orji Kalu ta ba su.
Ya kara da cewa idan har gwamnatin ta na nufin za ta kewaye kasuwar ta rusa gidajensu da kuma umartarsu koma wa kauyukan makwabta, hakan na nufi ta kore su ne a jihar.
Hausawa ‘yan kasuwar shanu sun roki Tinubu ya kawo dauki
Kun ji cewa, al’ummar Hausawa ‘yan kasuwar shanu a jihar Abia sun roki Shugaba Tinubu ya kawo mu su dauki.
Wannan rokon na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Abia ta umarce su da su tattara su bar kasuwar.
Asali: Legit.ng