‘Dan Shekara 30 Ya Zama Mai ba Gwamna Shawarar Tattalin Arziki a Arewacin Najeriya

‘Dan Shekara 30 Ya Zama Mai ba Gwamna Shawarar Tattalin Arziki a Arewacin Najeriya

  • Khalil Nur Khalil ya zama Mai ba Gwamnan jihar Katsina shawarwari a kan abubuwan da su ka shafi tattalin arziki
  • Matashin zai bar kujerarsa ta shugaban hukumar KADIPA a jihar Kaduna domin ya yi wa gwamnatin mahaifarsa aiki
  • Sabon Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi koyi da Malam Nasir El-Rufai wajen yin aiki da matasa a gwamnati

Katsina – Bayan watanni biyar a cikin ofis, Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina, ya jawo Khalil Nur Khalil a cikin gwamnatinsa.

Wata sanarwa da aka samu daga Mai taimakawa Gwamnan Katsina a kafofin sadarwa na zamani, Isah Miqdad, ta tabbatar da wannan.

A jiya Malam Isah Miqdad ya ce Mai girma Dikko Umaru Radda, PhD ya amince da nadin Khalil Nur Khalil a matsayin mai ba shi shawara.

Kara karanta wannan

Daga karshe Wike ya yi magana kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Khalil Nur Khalil
Gwamnan Katsina ya ba Khalil Nur Khalil mukami Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Dikko Radda ya ba Khalil Nur Khalil matsayi

Nur Khalil zai ba Gwamnan shawara ne a kan bangaren tatalin arziki da ya kware a kai, wa'adin aikinsa ya fara daga ranar 24 ga Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miqdad ya ce an haifi sabon Hadimin gwamnan ne a ranar 18 ga watan Nuwamban 1992 a Kaduna, amma asalinsa mutumin garin Bakori ne.

Khalil Nur Khalil ya rike KADIPA a Kaduna

Khalil ya samu digirin ilmin tattalin aziki daga jami’ar Eastern Mediterranean University da ke Cyprus inda ya gama da maki 3.98 cikin 4.

Kafin wannan nadin mukami da aka yi masa, matashin shi ne shugaban hukumar KADIPA da aka kafa domin jawo hannun jari a jihar Kaduna.

Khalil ya fara aiki a KADIPA a matsayin mai yi wa kasa hidima (NYSC) a 2018, har ya zama mai ba shugaban shawara, daga nan ya rike Darekta.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje Zai Yi Shari’a da Angwaye da Amaren da Hisbah Ta Aurar a Kano

Daga Darektan ne Nasir El-Rufai ya zabe shi ya zama shugaba, ya na ‘dan shekara 28.

Bayan aiki a Kaduna, Nur Khalil ya tafi gida

Kamar yadda ya fada a Twitter, an samu cigaba a KADIPA daga lokacin da ya karbi ragamar hukumar zuwa yanzu da ya yi ban-kwana.

Malam Khalil Nur Khalil ya godewa gwamnatin jihar Kaduna a kan damar da aka ba shi, ya na mai fatan wani zai daura a kan aikin da ya yi.

Gwamnatin Diko Radda da matasa

Kwanakin baya aka samu labari Mai girma Dikko Umar Radda ya ba Kwamred Muhammad Nuhu Nagaske mai shekara 26 mukami.

Baya ga haka, Gwamnan na Katsina ya ba Naufal Ahmed mai shekara 32 kujerar Darekta Janar na sashen fasahar zamani da aka kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng