Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Yan Sanda 3 a Wani Sabon Hari a Zamfara

Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Yan Sanda 3 a Wani Sabon Hari a Zamfara

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka jami'an ƴan sanda uku a wani ƙazamin hari da suka kai a jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan dai sun farmaki ƴan sandan lokacin da suke binciken ababen hawa a wani shingen bincike kan babban titin hanyar Funtua zuwa Gusau
  • Wani jami'an ɗan sanda ɗaya ya samu raunuka yayin da ba a san inda wasu ƴan sanda yan sanda biyar suke ba bayan sun yi ƙoƙarin tsira da rayukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Zamfara - An halaka ƴan sanda uku a wani hari da aka kai kan shingen binciken ababan hawa a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, ƴan sandan na gudanar da bincike ne a kan ababen hawa a babban titin hanyar Funtua zuwa Gusau a lokacin da ƴan bindigan suka kai farmaki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari a jihar Zamfara, sun yi awon gaba da mutum 5

Yan bindiga sun halaka yan sanda a Zamfara
Yan bindiga sun halaka jami'an yan sanda 3 a sabon farmaki a Zamfara Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Wani majiya ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An kashe ƴan sanda uku yayin da direban motar sintiri ta ƴan sandan da wasu ƴan sanda biyar suka shiga cikin daji domin tsira da rayukansu."
"Yayin da daga baya aka tsinci direban a sume a cikin daji inda aka garzaya da shi babban asibitin Tsafe, amma sauran ƴan sanda biyar ɗin ba a iya gano inda suke ba."

Majiyar ya ƙara da cewa, an kai harin ne a shingen binciken da ke ƙasa da kilomita 2 daga garin Tsafe da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

"Mun samu labarin cewa ƴan bindigan sun ajiye baburansu a gonakin da ke kusa da shingen binciken, sannan suka yi tattaki zuwa wajen inda suka kashe ƴan sanda uku." A cewarsa.

Ƴan sanda nawa ne a wajen?

Wani majiya ya bayyana cewa ƴan sandan da ke bakin aiki a lokacin harin sun kai mutum tara.

Kara karanta wannan

'Yan bautar ƙasa NYSC sun kuɓuta daga hannun yan bindiga, Sojoji da ƴan sanda sun yi namijin ƙokari

"Na wuce su ƴan mintoci kaɗan kafin harin da aka kai. Lamarin ya faru ne mintuna 30 bayan na wuce wurin binciken ababen hawan." A cewarsa.

Har yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar ba ta mayar da martani ba kan wannan mummunan harin da ƴan bindigan suka kai.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin garin Tsafe wanda ya tabbatar da aukuwar harin da ƴan bindigan suka kai kan jami'an ƴan sandan.

Malam Zaharaddeen ya bayyana cewa a yanzu ƴan bindiga sun addabi babbar hanyar Funtua-Gusau da kai hare-hare, inda ya ce ba su cika farmakar mutanen gari ba.

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Bakwai

A wani labarin kuma,.kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum bakwai a wasu ƙauyuka guda biyu na jihar Benue.

Ƴan bindigan sun halaka mutanen ne a ƙauyen Tse Gamber da kuma wani ƙauye kusa da Naka-Agagbe, duk a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng