Nesa Ta Zo Kusa: Ministan Tinubu Ya Bayyana Ranar da Za a Kammala Aikin Matatar Mai Ta Kaduna
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da lokacin kammala matatar mai da ke jihar Kaduna don samar da sauki ga ‘yan kasar
- Karamin ministan albarkatun mai a kasar, Heineken Lokpobiri ya ba da tabbacin bayan kai ziyarar gani da ido kan aikin matatar
- Ministan ya samu rakiyar shugaban kamfanin, NNPC, Mele Kyari da sauran mukarraban ma’aikatar don gane wa idonsu
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna – Karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya sanar da cewa za a karisa gyaran matatar mai ta Kaduna a karshen 2024.
Lokpobiri ya bayyana haka ne a yau Asabar 28 ga watan Oktoba yayin ran gadin duba aikin matatar, Legit ta tattaro.
Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Gwanjar da Barikokin ’Yan Sanda, Ta Bayyana Kwararan Dalilai
Wane alkawari ministan ya yi kan matatar Kaduna?
Ministan ya ce gwamnatinsu ta himmatu wurin samar da man a kasar ta hanyar dawo da matatun mai a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matatar ta Kaduna na daya daga cikin matattun matatun da ke kasar guda hudu wadanda su ke samar da man na tsawon shekaru.
Har ila yau, a watan Faburairu na wannan shekara, kamfanin NNPC ya rattaba hannu da wani kamfanin kasar Korea, Daewoo don gyaran matatun.
Yaushe ministan ya kai ziyara matatar Kaduna?
A ranar Asabar din, karamin ministan ya kai ziyara matatun don sanin halin da matatun ke ciki musamman na jihar Kaduna, Channels TV ta tattaro.
Ministan ya samu rakiyar shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari da wasu manyan mukarraban ma’aikatar da su ka mara mu su baya.
Daraktan gudanarwa na matatar ta Kaduna, Mustapha Sugungun ya jagoranci ministan da sauran mukarrabanshi zuwa matatar.
Kamfanin Dangote ya sanar da fara aikin tace danyen a matatarshi da ke jihar Legas a watan Oktoban wannan shekara.
Dangote ya sanar da ranar fara aiki a matatar mai da ke Legas
A wani labarin, Kamfanin Dangote ya sanar da ranar fara tace danyen mai a sabuwar matatar kamfanin da ke jihar Legas a kudancin Najeriya
Kamfanin ya sanar da cewa za su fara aikin ne a watan Oktoban shekarar 2023 wanda har lokacin ya wuce ba a fara yin wani abu ba.
'Yan Najeriya da dama sun caccaki kamfanin inda su ke dakon fara tace danyen man inda su ka nemi bahasi kan aikin matatar.
Asali: Legit.ng