Kotun Koli: Wani Gwamnan PDP Ya Sake Taya Shugaba Tinubu Murna

Kotun Koli: Wani Gwamnan PDP Ya Sake Taya Shugaba Tinubu Murna

  • Wani gwamna daga jam'iyyar adawa ta PDP ya sake taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar nasara a kotun ƙoli
  • Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya shiga cikin jerin gwamnonin jam’iyyar PDP da jiga-jigan jam'iyyar wajen taya shugaban ƙasa murna
  • Yayin da yake jawabi a wajen wani taro, gwamna Eno ya yi alƙawarin yin aiki tare da shugaban ƙasa

Uyo, Akwa Ibom – Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya taya Shugaba Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu a ƙotun ƙoli a kwanakin baya.

Ya jaddada cewa wannan nasara ta shari'a ta kawo karshen ƙararrakin da suka shafi zaɓen Shugaba Tinubu na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, rahoton The Punch ya tabbatar.

Gwamna Uno ya taya Tinubu murna
Gwamna Umo Eno ya taya Shugaba Tinubu murnar nasara a kotun koli Hoto: Umo Eno/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Duk da cewa jihar Akwa Ibom a al’adance jihar jam’iyyar PDP ce, gwamna Eno ya yi alƙawarin haɗa kai da gwamnatin Tinubu domin bunƙasa cigaba a jihar.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Bayyana a Karon Farko Bayan Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Kotun Ƙoli

Gwamna Eno ya bayyana haka ne a yayin wani taro na godiya tare da shugabannin addinin Kirista a jihar, wanda aka gudanar a dakin taro na Banquet dake gidan gwamnatin jihar dake Uyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma tabbatar wa ƙungiyar da himmarsa wajen jagorancin jihar Akwa Ibom ta kai ga ci domin tabbatar da amanar da coci da jama’a suka ba shi a lokacin zaɓen gwamna da aka yi kwanakin baya da suka wuce.

Gwamna Eno yayi alkawarin kawo cigaba a jihar Akwa Ibom

Gwamna Eno ya amince da ƙalubalen da al'ummar ƙasa ke fuskanta na cire tallafin man fetur amma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko wajen yin amfani da albarkatun da ake da su yadda ya kamata domin amfanin al'umma maimakon almubazzaranci da wasu abubuwan da ba su da muhimmanci.

A kalamansa:

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

"Lokacin da na ce babu kuɗi, ina nufin babu kuɗin ɓarnatarwa, amma akwai kuɗin yin abubuwa masu kyau. Akwai kudi don yin kowane abu mai kyau. Kuɗi domin saka hannun jari ba za su zama matsala a wannan jihar ba."
"Kuɗi su kansu kayan masarufi ne. Idan kuka ɓarnatar da kuɗi haka nan, za a rasa kimarsu."

Amaechi Ya Yi Magana Bayan Nasarar Tinubu a Kotu

A wani labarin kuma, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana bayan nasarar Shugaba Tinubu a kotun ƙoli.

Amaechi ya bayyana cewa babu wani abu da yake da muhimmanci a Najeriya sannan ƴan Najeriya ba su yi martani kan abubuwa masu muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng