“Ko Matata Aka Kama Cikin Yan Bindiga Zan Mika Ta Ga Hukuma”, Gwamna Radda
- Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ya sake jadadda aniyarsa na kin yin sulhu da yan ta’adda
- Radda ya ce jami’an tsaro za su dunga bin yan bindiga mabuyarsu a dazuzzuka maimakon jiran su kai hari kafin a far masu
- Gwamnan na APC ya kuma sha alwashin cewa ko matarsa ce aka samu da hannu a ta'addanci, zai mika ta ga jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya jaddada cewar babu wani sulhu da zai yi da yan ta’adda kuma cewa cin kashin da suke yi a jihar ta isa haka.
Da yake jawabi ga manema labarai, Radda ya bayyana cewa ko na kusa da shi aka samu a ta’addancin da ke faruwa a jihar zai dandana kudarsa, rahoton Rfi Hausa.
Radda zai dauki mataki kan yan bindiga
Ya kuma sha alwashin cewa za su kai yan ta’adda hari har mabuyarsu a cikin jeji ba wai sai sun jira har an kawo masu hari ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A karshe gwamnan ya ce ko matarsa ce aka samu tana da alaka da ayyukan ta'addanci toh sai ta fuskanci hukunci, domin a cewarsa alfarma ce ta kashe kasar nan.
Ya ce:
“Na fadi na sake fadi cewa ba zan yi sulhu da yan bindiga ba.
“Barawo barawo ne, dan ta’adda dan ta’adda ne, me kashe mutane me kashe mutane ne, mu za mu yi maganin shi. Kai bari in gaya ma wani abu wallahi tallahi ko matata aka kama tana da hannu da yan ta’addan nan wallahi tallahi zan mika ta hannun jami’an tsaro.
“Ba za mu yarda da wannan abun ba, wannan abun shi ya kashe kasarmu baki daya, alfarma ita ta kashe kasarmu, kamata ya yi doka ta yi aiki. Mu ma yanzu mun shirya za mu dunga iske su gidajensu da lungunansu a cikin dajin muna cin masu. Mu ma ba za mu kwanta ba mu jira har sai wani ya kawo mana hari ba."
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wata mazauniyar jihar Katsina kan matakan da Gwamna Radda ke dauka don kawo karshen yan bindiga a jihar.
Malama Amina Funtua ta ce lallai da alama wanka zai biya kudin sabulu a wannan gwamnati. Ta ce suna sanya ran samun gagarumin ci gaba a wannan gwamnati ta bangarori daban-daban.
Ta ce:
“Ba mu da abun da za mu ce sai Alhamdulillah, ga dukkan alamu Allah ya amsa addu’o’in bayinsa. Duba ga salon da sabon gwamna mai ci ya dauko muna kyautata zaton samun sauyi a musamman a bangaren tsaro.
“Muna goyon bayan wannan mataki da gwamnan ya dauka na cewa ba zai yi sulhu da yan bindiga ba. Na baya da aka yi me hakan ya haifar mana idan ban da danasani da cutuwa. Mu dai abun da za mu yi shine za mu ci gaba da taya Dikko Raddanmu da addu’o’in samun nasara a duk ayyukan alkhairi da zai sa a gaba.”
Yan bindiga: Zan sadaukar da raina, Radda
A fege guda, mun ji a baya cewa Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin kawo karshen ayyukan ta'addancin yan bindiga a jihar.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Gwamna Raɗɗa ya ce tsaro shi ne abu mafi muhimmanci kuma bisa haka ne ya kafa dokar kirkiro da rundunar tsaron jiha, waɗanda aka ba su makamai.
Asali: Legit.ng