'Yan sanda sunyi nasarar kama wani gawurtacen mai garkuwa da mutane a Zamfara
- Jami'an yan sanda na jihar Zamfara sunyi ram ta wani gagarumin mai garkuwa da mutane wanda akafi sani da Gaugai
- An kama shi ne a ranar 1 ga watan Janairun 2018 a kusa da kauyukan Kunkeli da Chabi da ke karamar hukumar Maru
- A halin yanzu yana taimakawa jami'an tsaro da bayanai kan yadda zasu kamo sauran yan kungiyar tasu da masu garkuwa da mutane da sata
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu yace rundunar tayi nasarar cafke wani gagarumin mai satan shanu da garkuwa da mutane mai suna Musa Abdullahi wanda akafi sani da Gaugai.
Shehu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya baiwa manema labarai ranar Laraba a Gusau. Jami'an Operation Sharar Daji ne suka kama Gaugai a ranar 1 ga watan Janairun 2018 a kusa da kauyen Kunkeli da Chabi da ke karamar hukumar Maru na jihar ta Zamfara.
KU KARANTA: Assha! Directa a jihar Kogi ya rasu bayan sallamar sa daga aiki
An sami Gaugai dauke da bindiga kirar AK 47 guda daya da kuma harsashi da dama. Shehu ya kara da cewa Gaugai yana taimakawa rundunar da bayyanai kan yadda za'a taso keyar sauran abokanan aikata banar tasa daga bisani kuma za'a kai shi kotu domin ya fuskanci hukunci.
Kamfanin dilancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa wanda ake tuhuma din yana cikin gagan wasu masu garkuwa da mutane ne wanda yan sanda ke nema ruwa a jallo domin sun dade suna fitinar al'ummar jihar ta Zamfara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng