An Fara Sauraran Shari'ar Kisan Gillar da Aka Yi Wa Janar Alkali a Kotun Tarayya da Ke Jos

An Fara Sauraran Shari'ar Kisan Gillar da Aka Yi Wa Janar Alkali a Kotun Tarayya da Ke Jos

  • A watan Satumban 2018 wasu matasa sun yi wa babban soja kisan gilla a karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar Plateau
  • Marigayin Manjo-Janar Idris Alkali ya rasa ransa ne yayin da ya ke tafiya zuwa Bauchi daga birnin Tarayya Abuja
  • Daga bisani a watan Nuwamban shekarar 2018, rundunar sojin Najeriya ta umarci yashe rijiyar tare da tsamo gawar marigayin a kauyen Guchwet

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Plateau - Kotu ta fara sauraran shaidu kan shari'ar kisan gilla da aka yi wa Janar Idris Alkali a jihar Plateau.

Babbar kotun da ke zamanta a jihar na ci gaba da sauraran karar ce da safiyar yau Laraba 25 watan Oktoba inda ake zargin mutane 21 da kisan gillar.

An fara sauraran shaidu kan shari'ar kisan gillar Manjo-Janar Alkali a Jos
Marigayi Janar Alkali da aka kashe a garin Jos. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Yaushe aka hallaka marigayin, Janar Alkali a Jos?

Har ila yau, wakilan rundunar sojin Najeriya ta hallara a babbar kotun wanda ita ce ta shigar da kara kan kisan gillar sojan, cewar Aminiya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Yankewa Shahararren Likita Da Ya Lalata Yar’uwar Matarsa Daurin Rai Da Rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a mantaba, an hallaka Manjo-Janar Alkali ne a watan Satumban shekarar 2018 yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga birnin Tarayya Abuja.

Daga bisani a watan Nuwamban 2018 aka tsinci gawar marigayin a cikin wata tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Rundunar tun farko ta umarci yashe ruwan rijiyar inda ta yi nasarar tsamo gawar tare da daukar ta zuwa asibiti don bincike.

Legit Hausa ta tattaro cewa daga baya an kama wanda ake zargi da hannu wurin kisan gillar da ka yi wa Janar Alkali a watan Janairun 2020.

Tun farko, a watan Nuwamban 2019, an kama wasu mutane biyu da hannu cikin kisan sojan da su ka hada da Chuwang Samuel da Nyam Samuel.

An nemi fitaccen soja an rasa a garin Jos

Kara karanta wannan

Jerin Manyan 'Yan Takara 5 da Jam'iyyun da Za Su Fafata a Zaben Jihar Kogi a Wata Mai Kamawa

A wani labarin, an samu rahoto mai tayar da hankali bayan batan dabon wani soja mai suna Manjo-Janar Alkali Idris Mohammed a garin Jos na jihar Plateau.

Kungiyar rajin tabbatar da dimukradiyya da samar da shugabanci na gari, CUPS ita ta fara sanar da haka a kafofin sadarwa.

Sojin wanda ya bace dai ana hasashen ya na kan hanyarsa ce ta zuwa Bauchi daga birnin Tarayya Abuja lokacin da iftila'in ya afku a Jos ta Kudu da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.