Gwamna Adeleke Na Jihar Osun Ya Kafa Dokar Hana Jami’an Gwamnati Fita Kasashen Waje

Gwamna Adeleke Na Jihar Osun Ya Kafa Dokar Hana Jami’an Gwamnati Fita Kasashen Waje

  • Yayin da gwamnatoci ke fama da rashin kudade, gwamnatin jihar Osun ta kafa tsatssaurar doka kan jami’an gwamnati kan yawace-yawace
  • Gwamna Ademola Adeleke shi ya sanar da haka inda ya ce daga yanzu har zuwa karshen shekara ya haramta fita kasashen waje
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar na fama da karancin kudade wanda ya yi sanadin soke bikin ranar ‘yanci a jihar

Jihar Osun – Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya soke fita kasashen waje ga dukkan mukarraban gwamnatinsa a jihar.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne don rage yawan kashe kudade ganin yadda jihar ke fama da karancin kudi a halin yanzu, cewar The Nation.

Gwamna Adeleke na Osun ya haramta fita kasashen ketare ga jami'an gwamnati
Gwamna Adeleke ya kafa dokar hana fita kasashen ketare. Hoto: Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

Wace doka gwamna Adeleke ya kafa a Osun?

Adeleke ya ce dokar za ta fara aiki ne daga yanzu har zuwa karshen wannan shekara inda ya ce sai dai idan akwai fita ta gaggawa.

Kara karanta wannan

Babban Kuskuren Da Tinubu Ya Ke Tafkawa, Ya Haddasa Tashin Dala a Yau - Masani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ademola ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa, Olawale Rasheed a yau Litinin 23 ga watan Oktoba a Ibadan.

Sanarwar ta ce:

“Duk wasu yawace-yawace zuwa kasashen ketare an dakatar da su har zuwa karshen shekara sai dai idan ya zama dole ko kuma da umarnin Gwamna.
“Dole mu kiyaye hakan don rage yawan kashe kudade a gwamnati da wasu kare-kare na bayan fage.”

Meye dalilin kafa dokar ta Adeleke a Osun?

Ya kara da cewa:

“Bukatunmu a ofisoshi zuwa wuraren kwana su na da yawa amma kuma mu na da karancin kudade, ya zama dole mu samar da wata hanya don inganta hakan.”

Ya ce dole wadanda abin ya shafa su yi hakuri zuwa wani lokaci da za a samu sauki da kuma yalwatuwar kudade a jihar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Jihar Osun na fama da karancin kudade wanda hakan ne ma ya saka gwamnan jihar soke bikin ranar ‘yanci don tsuke bakin aljihu.

Gwamnatin Osun ta soke bikin ranar ‘yanci

A wani labarin, Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya soke bikin ranar samun ‘yancin kan Najeriya a jihar.

Gwamnan ya kirayi al’ummar jihar da su yi amfani da ranar wurin addu’ar samun zaman lafiya a kasa baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.