Gwamnatin Jihar Borno Ta Haramta Barace-Barace da Zaman Banza

Gwamnatin Jihar Borno Ta Haramta Barace-Barace da Zaman Banza

  • Gwamnatin jihar Borno ta haramta barace-barace da zaman banza a wasu yankunan jihar da ke Arewacin Najeriya
  • Rahoto ya bayyana wuraren da gwamnati ta hana wadannan dabi'u masu kawo koma-baya ga al'umma
  • Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fuskantar barace-barace da ke kaiwa ga ayyukan ta'addanci

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta haramta barace-barace a kan tituna a ciki da wajen birnin Maiduguri da karamar hukumar Jere, rahoton Leadership.

Haramcin na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tar ya fitar a ranar Lahadi a Maiduguri.

Gwamnan Borno ya hana Bara a jiharsa
An haramta Bara a Borno | Hoto: Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Sako daga gwamantin Borno

Sanarwar ta kuma bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Barace-barace a kan tituna da zaman banza ba sa daga cikin halinmu a Borno. Mu mutane ne masu daraja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Fara Bincike Bayan Sabon Kwamishina Ya Yi Mutuwar Bazata

“Muna sanar da jama’a cewa gwamnatin jihar Borno ta sanya dokar hana fita a duk wani nau'in barace-barace da zaman banza a tsakanin garin Maiduguri da kewaye da karamar hukumar Jere.
“Haramcin ya shafi wurare kamar haka: Dukkan gine-ginen gwamnati, duk wasu wuraren ibada, duk wasu cibiyoyin kasuwanci, Sakatariyar Musa Usman, Kasuwar Monday, Tsohuwar Kasuwar Maiduguri, Kasuwar Budum, Titin Legas, Unguwar Kwastam, yankin Ofishin Wasiku, Mahadar Galadima , Mahadar Kwamishinan ‘yan sanda, titin Damboa, titin Baga, titin Dandal da sauransu.”

Yaushe dokar za ta fara aiki?

A cewar sanarwar, haramcin ya fara ne da nan take kuma za a dauki mataki kan wadanda suka ketare umarnin gwamnatin jihar, Within Nigeria ta tattaro.

Ba jihar Borno kadai ke fuskantar barace-barace ba, kusan dukkan jihohin Najeriya ne ke cikin wannan hali, to amma meye tanadin gwamnati na yaki da zaman banza?

An farmaki gwamnan jihar Kogi

Kara karanta wannan

Sabon Kwamishina Da Aka Nada a Kwanakin Nan Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, An Bayyana Dalilin Mutuwarsa

A wani labarin, gwamnatin jihar Kogi a ranar Lahadi ta ce jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kisa da aka yiwa gwamnan jihar Yahaya Bello, The Nation ta ruwaito.

A cewar gwamnatin, an farmaki gwamnan ne a jiharsa da ke da tazarar kilomita kadan da babban birnin tarayya Abuja, a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki daga birnin Lokoja.

Sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar a Abuja, ya ce an kai harin ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel