Ana Hasashen Matatar Dangote Za Ta Kawo Tsadar Mai da Zarar Ya Fara Aiki a 2024

Ana Hasashen Matatar Dangote Za Ta Kawo Tsadar Mai da Zarar Ya Fara Aiki a 2024

  • Rahoton EIU ya sanar da cewa fara aiki a matatar Dangote zai iya kara tashin farashin man fetur a kasar a shekarar 2024
  • Rahoton ya kuma ce babban matatar wanda ta kai girman 650,000 zai kawo karshen shigo da mai na NNPC da sauran ‘yan kasuwa
  • Matatar ana sa ran za ta fara fitar da bakin mai da mai din jirgin sama a watan Oktoba da kuma man fetur a watan Nuwamba

Yayin da ake kokarin fara aiki a matatar Dangote, rahotanni sun tabbatar da cewa hakan zai kara tsadar man fetur a kasar.

Ana sa ran fara aiki a matatar zai kawo karshen shigo da man fetur da kuma sauran sinadarai a shekarar 2024, Legit ta tattaro.

Matatar Dangote na iya jawo tashin farashin mai a Najeriya
Matatar Dangote za ta fara fitar da bakin mai a wannan wata. Hoto: Dangote, Anadolu Agency.
Asali: Getty Images

Meye rahoton ya ce kan matatar Dangote?

Rahoton Economic Intelligence Unit (EIU) ya yi hasashen samun karuwa a fitar da danyen mai daga ganga miliyan 1.12 a 2022 zuwa miliyan 1.4 a ko wace rana.

Kara karanta wannan

Babban Kuskuren Da Tinubu Ya Ke Tafkawa, Ya Haddasa Tashin Dala a Yau - Masani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya bayyana hakan ne bayan ganin sauye-sauye da aka samu a bangaren man fetur a kasar a ‘yan kwanakin nan.

Daga cikin lamuran da su ka faru akwai shirin karisa matatar Dangote da daidaito a yankin Neja Delta da kuma mayar da kamfanin NNPC ga ‘yan kasuwa.

Me ake hasashe kan farashin mai?

Rahoton ya kara da cewa Najeriya za ta sauya farashin man fetur musamman idan kamfanin ya fara fitar da kaya a shekarar 2024.

A baya, kamfanin BUA ya rage farashin siminti wanda hakan ya sanya ‘yan kasar ke kalubalantar Dangote da shi ma ya bi sahun mai kamfanin BUA.

An yi ta yada jita-jita cewa shi ma Dangote ya rage farashin siminti a Najeria zuwa Naira 2,400.

Dangote ya karyata jita-jitar da ake cewa ya rage farashin siminti bayan BUA ya rage na shi a farkon wannan wata.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Kamfanin Sukarin Dangote zai dauki ma’aikata dubu 300

A wani labarin, Kamfanin sukarin Dangote ya sanar da daukar ma’aikata 300,000 don rage yawan zaman banza a kasar.

Kamfanin ya ce duk shekara ya na daukar mutane dubu 7 a iya kamfanin sukarin Dangote da ke Numan a jihar Adamawa.

Manajan ayyuka a kamfanin, Bello Dan Musa ya bayyana cewa dubban mutane ne ke aiki a kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.