Hukumar NSCDC Ta Kama Dalibin Ajin Karshe a Jami’ar ABU da Kisan Kai a Jihar Bauchi
- Hukumar NSCDC a jihar Bauchi ta kama wani dalibin Jami’ar ABU kan zargin kisan kai a jihar
- Wanda ake zargin, Abdullahi Ibrahim ya hallaka wani yaro Umar Usman mai shekaru 17
- Kwamandan hukumar, Ilelaboye Oyejide shi ya tabbatar da haka yayin ganawa da manema labarai
Jihar Bauchi – Jami’an hukumar NSCDC a jihar Bauchi sun cafke wani dalibin Jami’ar ABU da ke kan zargin hallaka wani matashi mai shekaru 17 a jihar.
Wanda ake zargin Abdullahi Ibrahim ya na ajin karshe a tsangayar kula da lafiyar dabbobi ya kashe Umar Usman har lahira.
Meye NSCDC ke zargin dalibin da aikatawa?
Kwamandan hukumar a jihar, Ilelaboye Oyejide shi ya tabbatar da haka yayin ganawa da manema labarai a jiya Lahadi 22 ga watan Oktoba, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyejide ya ce an kama Abdullahi ne a karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi bayan samun mamacin a cikin tsumma a bayan gari.
Ya ce:
“Wannan matsala ce ta kisa bayan samun gawar Umar Usman a cikin tsumma a yashe a bayan garin Misau a ranar 20 ga watan Oktoba.
“An yi gaggawar daukarshi zuwa babban asibitin Misau inda aka tabbatar da cewa ya mutu sannan aka mika shi ga ‘yan uwansa don binne shi.”
Meye martanin wanda hukumar NSCDC ke zargi?
Kwamandan ya ce bayan kwakkwaran bincike, hukumar ta kama dalibin ajin karshe a Jami’ar ABU da ke Zaria, Abdullahi Ibrahim, Daily Post ta tattaro.
Ya kara da cewa:
“Mun gano cewa a cikin tattaunawa da su ka yi tsakanin wanda ake zargin da marigayin, Abdullahi ya nemi yin luwadi da tura masa hotonsa tsirara.
“Bayan marigayin ya je ya same shi, sai wanda ake zargin ya caka masa wuka a ciki inda ya saka shi a cikin tsumma tare da jefar da shi.”
A martaninshi, wanda ake zargin ya ce yaron ne ya zaro masa wuka zai kashe shi, dalilin haka ya yi kokarin kare kansa.
‘Yan sanda sun kama mata da kisan kai a Bauchi
Kun ji cewa, ‘yan sanda a jihar Bauchi sun cafke mata da zargin kashe ‘yar kishiyarta a jihar.
Wacce ake zargin mai suna Khadija Adamu ta roki afuwa a wurin hukumomi inda ta ce ba da gan-gan ta yi ba.
Asali: Legit.ng