Fasto Odumeji Ya Yi Barazana Ga Fastocin Najeriya da Ke Yi Wa Isra’ila Addu’a
- Fasto Chukwuemeka Odumeji ya yi barazana ga Fastocin Najeriya da ke bata lokacinsu wurin yi wa kasar Isra’ila addu'a
- Faston ya ce zai mayar da su makafi kuma kurame duk lokacin da su ka sake yi wa Isra’ila addu’a inda ya ce Najeriya tafi bukatar addu’a
- Odumeji ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 22 a watan Oktoba yayin gabatar da hudubar coci a cikin wani faifan bidiyo da aka yada
Shahararren Fasto mai suna Chukwuemeka Odumeji ya girgiza intanet bayan yin barazana ga Fastoci ma su yi wa Isra’ila addu’a.
Odumeji ya bayyana haka ne a cikin hudubar ranar Lahadi 22 ga watan Oktoba a coci inda ya ke magana kan rikicin Isra’ila da Gaza, Legit ta tattaro.
Wane barazana Faston ya yi wa ma su addu’a ga Isra’ila?
Faston ya yi barazanar mayar da Fastoci da ke addu’a ga Isra’ila makafi da kurame inda ya ce ba su san ciwon kansu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa Najeriya tafi ko wace kasa bukatar addu’a idan aka kwatanta da Isra’ila inda ya ce tafi ko wace kasa shiga tashin hankali.
Wannan barazana na Faston na zuwa ne mako guda bayan Fasto Enoch Adeboye ya yi addu’a ta musamman ga Isra’ila.
Meye mutane ke cewa kan barazanar Fasto kan Isra’ila?
Mutane sun yi martani kan barazanar Faston:
@jakyosaretin:
“Duk ranar da ka yi barazana ga Adeboye za ka gane kurenka, ka ci gaba da yaudarar mutane.”
@zainab_ayoo:
“Wannan mutumin na kama da Bobrisky wani lokaci idan ya tsufa.”
@soulbeat:
“Ba ka yi wa shugaban kasarka addu’a ba da bai san hagu da dama ba.”
@jst_bryan:
"Meye za ka yi wa Fasto Adeboye da ya mu su addu'a wancan makon."
Fasto ya yi wa Isra’ila addu’ar samun nasara
A wani labarin, shahararren Fasto Enoch Adeboye ya yi addu’a ta musamman ga kasar Isra’ila yayin da su ke yaki da kungiyar Hamas.
Faston ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta karade kafofin sadarwa inda ya bukaci addu’ar samun nasara ga Isra’ila yayin rikicin.
Wannan na zuwa ne yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare kan Gaza.
Asali: Legit.ng