Jami'an NSCDC Sun Cafke Yan Luwadi Na Shirin Auren Jinsi a Gombe

Jami'an NSCDC Sun Cafke Yan Luwadi Na Shirin Auren Jinsi a Gombe

  • Hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) ta samu nasarar cafke wasu ɓata gari masu aikata luwaɗi da ke shirin gudanar da auren jinsi a jihar Gombe
  • Jami'an hukumar ne dai suka yi musu dirar mikiya yayin da suke shirye-shiryen gudanar da auren jinsin a wajen bikin ranar haihuwar ɗaya daga cikinsu
  • A wajen bikin an cafke mutum 59, inda mutum 21 suka amsa cewa su ƴan luwaɗi ne, sannan za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike

Jihar Gombe - Jami'an hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC), sun daƙile wani shiri da wasu mutane suka yi na gudanar da auren jinsi a jihar Gombe.

Jaridar The Punch ta ce jami'an hukumar sun kuma cafke mutum 76 waɗanda ake zargin suna da hannu dumu-dumu a shirin gudanar da auren jinsin.

Kara karanta wannan

Rayuka da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota da Ya Auku a Kan Babban Titi a Najeriya

An cafke masu shirin auren jinsi a Gombe
Wasu daga cikin wadanda aka cafke Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Buhari Sa’ad ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a gaban ƴan jarida, a hedikwatar hukumar da ke Gombe, a madadin kwamandan hukumar na jihar, Mohammed Muazu.

Ya bayyana cewa daga cikin mutum 76 da ake zargin, mutum 59 maza ne yayin da mutum 21 suka amsa cewa suna aikata luwaɗi, inda ya ce an kuma kama mata 17 a wurin da lamarin ya faru, rahoton Tribune ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"An kama su ne a Duwa Plaza da ke kan titin Bauchi zuwa Gombe a lokacin da suke gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar wani ɗan luwaɗi, kuma suna shirin yin auren jinsi kafin mutanenmu su kai farmaki wurin."
"An kama maza mutum 59, mutum 21 daga cikinsu sun amsa cewa su ƴan luwaɗi ne, sannan an cafko mata 17 da ke a wurin."

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Wadanda Ake Zargi da Kisan Diyar Dan Majalisa

"Za a gurfanar da su gaban kotu domin amsa laifin da suka aikata wanda babban laifi ne a jihar Gombe."

An Kori Ma'aikaciya Daga Wurin Aiki Kan Kwanciya da Maza

A wani labarin na daban kuma, wata ma'aikaciya a ƙasar Australia ta rasa aikinta bayan an gano ta kwanta da maza sama da 300.

Annie Knight mai shekara 26 a duniya ta rasa aikin nata ne bayan an gano lalatar da take yi a shafinta na Onlyfans.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng