Jami’an Tsaro Sun Yi Nasarar Cafke ’Yan Fashin Bankuna a Jihar Benue Bayan Artabu
- Rundunar ‘yan sanda da jami’an sojoji da saura sun yi nasarar kama ‘yan fashi hudu da ake zargi da fashin bankuna a jihar Benue
- ‘Yan fashin sun kai harin ne a jiya Juma’a 20 ga watan Oktoba a Otukpo da ke jihar inda su ka hallaka ‘yan sanda uku yayin harin
- Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene ta bukaci ‘yan jaridu da su dakata har sai an kammala bincike tukun
Jihar Benue – Gamayyar jami’an tsaro sun yi nasarar kama mutane hudu da ake zargi da fashin bankuna a jihar Benue.
A jiya Juma’a 20 ga watan Oktoba ne aka aiwatar da fashin yayin da jami’an ‘yan sanda uku su ka rasa ransu., Premium Times ta tattaro.
Meye ake ciki kan kama 'yan fashin a Benue?
Wata majiya daga hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin bayan ta yada bidiyon wadanda ake zargin ga Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce:
“An kama ‘yan fashin guda hudu a kan hanyar Otukpo zuwa Taraku a jihar Benue a yau Asabar 21 ga watan Oktoba.
“Yan fashin na daga cikin wadanda su ka kai farmaki bankuna da ofishin ‘yan sanda a Otukpo da ke jihar Benue a jiya Juma’a 20 ga watan Oktoba.”
Meye martanin 'yan sanda kan 'yan fashin a Benue?
Yayin da aka tuntubeta, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene ta bukaci ‘yan jarida da su jira a kammala bincike tukun, cewar TheCable.
Ta ce:
"Ku barsu su yi aikinsu na bincike idan sun gama za su ba da rahoto."
Tun farko, rundunar ta tabbatar da cewa 'yan fashin guda biyu sun rasa ransu yayin arangama.
Ta kuma tabbatar da cewa jami'an tsaro uku sun rasa rayukansu da wani DPO guda daya yayin harin da aka kai a jiya Juma'a 20 ga watan Oktoba a jihar.
Yan sanda sun kama matar da ta hallaka 'yar kishiyarta
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wata mata da zargin kashe 'yar kishiyarta saboda ta yi kashi a jikinta.
Wacce ake zargin mai suna Khadijah Adamu 'yar kimanin shekaru 18 ta ce ba da gan-gan ta aikata hakan ta yi ne kawai don gyara.
A karshe ta nemi afuwar hukumomi inda ta ce iyayen yarinyar sun riga sun yafe mata kuskuren da ta aikata.
Asali: Legit.ng