Kishi: Yadda wata mata ta tura kishiyarta cikin rijiya

Kishi: Yadda wata mata ta tura kishiyarta cikin rijiya

- Wata mata mai suna Hauwa Lawan ta hankada kishiyarta goye da danta a baya cikin rijiya

- Wannan mummunan lamarin ya auku ne a kauyen Rurum dake karamar hukumar Rano ta jihar Kano

- Bayan an garzaya da Zuwaira asibiti, babu dadewa tace ga garinku, amma a halin yanzu Hauwa ta shiga hannun 'yan sanda

Wata mata mai suna Hauwa Lawan mai shekaru 30 a garin Rurum, ta tura kishiyarta cikin rijiya tare da goyonta.

Hauwa ta tura Zuwaira ne da ke goye da Mustafa mai shekara daya da rabi cikin rijiya.

A yayin da rundunar ‘yan sanda suka samu labarin wannan aika-aikar, sai suka gaggauta kai dauki zuwa garin Rurum inda suka tsamo Zuwaira daga rijiyar. Zuwaira bata dade a asibiti ba kuwa tace ga garinku.

Amma Allah cikin ikonsa sai Mustafa ya tsallake wannan lamarin don kuwa ya rayu.

DUBA WANNAN: Zargin kisan kai a Kano: Kotu ta ba dan bautar kasa masauki a gidan gyaran hali

Bayan aukuwar mummunan lamarin, Hauwa Lawan ta gudu. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan. Ya ce kwamishinan ‘yan sandar jihar ya bayar da umarnin a cafko Hauwa a duk inda take.

Da misalin karfe daya da minti goma sha bakwai na daren ne kuwa ‘yan sanda suka kamo Hauwa Lawan.

DSP Abdullahi Haruna, yace kwamishinan yan sandan na jihar Kano, Habu Sani ya bayar da umarnin a mika korafin zuwa babban sashin bincike na kisan kai, dake rundunar ‘yan sanda a Bompai domin fadada bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel