An Gurfanar Da Malamin Makaranta Da Wasu 5 Kan Laifin Sata a Osun

An Gurfanar Da Malamin Makaranta Da Wasu 5 Kan Laifin Sata a Osun

  • Jami'an NSCDC da ma'aikatan hukumar rarraba lantarki na Osun sun kama wasu da laifin shan lantarki ta haramtaciyyar hanya
  • Daga cikin wadanda aka kama akwai wani malamin makaranta mai suna John da wasu mutanen biyar duk a garin Osogbo
  • John ya amsa cewa ya aikata laifin amma mitarsu ce ta lalace ba su iya loda kati kuma wanda ya saba loda musu kai tsaye baya nan

Osun - Rundunar Tsaro NSCDC reshen Jihar Osun, a ranar Litinin, ta yi holen wani malamin makaranta mai zaman kanta, da aka ce sunansa John da wasu mutane biyar, kan lalata mitar lantarki na nufin amfani da wuta na bulus.

Sauran wadanda ake zargin sun hada da Jaye Abayomi, Abidemi Enoch, Jackson Imukodro, Adeleke Fatima da Azeez Mutiu, rahoton The Punch.

An kama malamin makaranta da wasu 5 kan satar lantarki
Malamin makaranta ya shiga hannu kan sata a Osun. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Da ya ke gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar NSCDC, Kwamandan Rundunar, Mr Sunday Agboola, ya ce an kuma dukkan wadanda ake zargin ne a Awosuru, Alekuwodo, Jaleyemi, Ogo Oluwa da Omigade - duk a yankin Osogbo.

Kara karanta wannan

Ruwan Nadin Mukaman Tinubu Ya Shiga SON, An Nada Sabon Shugaba a Najeriya

Shugaban na NSCDC ya kara da cewa jami'an rundunar ne suka kama wadanda ake zargin yayin wani atisayen hadin gwiwa da ma'aikatan kamfanin lantarki na Ibadan a ranar 13 ga watan Okotoban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina takaicin yadda mutane ke cigaba da satar lantarki a Osun - Kwamandan NSCDC

Agboola wanda ya ce an yi kamen ne domin su zama izina ga mutanen gari da ke niyyar satar lantarki, ya koka cewa mutane da dama a jihar na cigaba da aikata laifin.

Ya ce:

"Kwamandan yana takaici. Duk da yawan kame da aka yi don zama darasi ga mutanen da ke laifin, wasu har yanzu sun ki dena wa.
"NSCDC ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai mun ga canji na gari a jiharmu. Bayan kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu."

Kara karanta wannan

Kano: An Kama Mutum 30 Kan Yunkurin 'Tayar da Tarzoma' a Wurin Auren Gata 1,800, Sun Yi Bayani

Malamin makarantan ya fadi dalilin da yasa shi satar lantarki

Da ya ke magana da Punch, John ya amsa cewa ya cire lantarkin gidansa daga kan mita, yana mai cewa:

"Wurin saka katinmu ya lalace kuma muna da wani jami'i da ke saka mana kati kai tsaye amma baya nan ranar Juma'a don ya saka mana, shi yasa na dora wutar kai tsaye."

An gurfanar da matashi a kotu kan satar karafa a makabarta

A wani rahoton, Kotun Majistare da ke Ikeja, Jihar Legas ta yanke wa wani matashi daurin shekara 28 a gidan gyaran hali.

Ana zargin matashin ne da satar karafa wadanda ake amfani da su don rufe mamata a makabarta a jihar Legas, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164