Sabon Kwamishina a Jihar Borno Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Yau Asabar
- Ana cikin jimami yayin da sabon kwamishina a rasa rayuwarsa a jihar Borno da safiyar yau Asabar
- Marigayin mai suna Injiniya Ibrahim Garba ya rasa ransa ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri, UMTH
- Rahotanni sun tabbatar da cewa guba ne sanadin mutuwar sabon kwamishinan na jihar Borno
Jihar Borno - Allah ya yi wa sabon kwamishinan gyara da sake matsuguni a jihar Borno rasuwa da safiyar yau Asabar.
Marigayin Injiniya Ibrahim Idris Garba ya rasu ne a gidansa da ke rukunin gidajen 777 a Maiduguri, babban birnin jihar, Legit ta tattaro.
Menene sanadin mutuwar kwamishinan a Borno?
Ibrahim wanda ya samu mukamin kwamishinan a kwanakin nan ya rasu a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri (UMTH).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ZagazOlaMakama ya tabbatar da mutuwar kwamishinan a shafin Twitter inda ya ce guba ne sanadin mutuwarshi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu da safiyar yau Asabar 21 ga watan Oktoba a Maiduguri.
Sanarwar ZagazOlaMakama ta ce:
"An yi babban rashi yayin da sabon kwamishinan ayyuka, gyara da sake matsuguni a jihar Borno ya rasu.
"Ya rasu a gidansa da ke rukunin gidajen 777 da ke Maiduguri, an sanar da mutuwarshi a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri.
"Ana kyautata zaton guba ce ta yi ajalinshi."
Wane mukami marigayin ke rike da shi a Borno?
Sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne sanadiyyar ciwon zuciya da yake fama da shi.
Marigayin bayan mukamin kwamishina, ya kasance hadimin Gwamna Babagana Zulum a bangaren kula da ayyuka.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba mu samu martan daga gwamnatin jihar ba kan wannan babban rashi na sabon kwamishinan a jihar.
Dattijuwa Ta Rasa Ranta Bayan 'Yan Ta'adda Sun Yi Mata Yankan Rago a Jihar Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Martani
'Yan Kalare sun yi wa wata mata yankan rago a Gombe
A wani labarin, wasu da ake zargin 'yan Kalare ne sun yi ajalin wata dattijuwa mai shekaru 58 a jihar Gombe.
Marigayiyar mai suna Aishatu Abdullahi da aka fi sani da 'Adda Damori' ta rasa ranta bayan an yi mata yankan rago a gidanta.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Mahid Mu'azu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun fara gudanar da bincike kan kisan gillar.
Asali: Legit.ng