Dakarun Sojojin Najeriya Sun Sheke Yan Ta'adda 37 a Mako 1

Dakarun Sojojin Najeriya Sun Sheke Yan Ta'adda 37 a Mako 1

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar murƙushe ƴan ta'adda 37 a sassa daban-daban na ƙasar nan
  • Sojojin sun kuma cafke wasu mutum huɗu masu taimakawa ƴan bindiga a jihohin Borno da Benue
  • Dakarun sojojin sun kuma cafke ƴan ta'adda 95 cikin mako ɗaya a sassa daban-daban na ƙasar nan

FCT, Abuja - Dakarun sojoji na rundunar ‘Operation Hadin Kai’ da ‘Whirl Stroke’ sun kama wasu masu taimakawa ƴan ta'adda mutum huɗu a jihohin Borno da Benue.

An kama su ne a wasu ayyuka daban-daban da aka gudanar tsakanin ranakun 9 zuwa 11 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton jaridar The Punch.

Sojoji sun halaka yan ta'adda 37
Dakarun sojoji sun samu galaba kan yan ta'adda Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Wata sanarwa a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, ta bakin kakakin hukumar tsaro ta ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, ya nuna cewa bayan bincike da aka yi, an kama wasu mutum uku da suke taimakawa ƴan ta'adda karɓar kuɗin fansa a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Arewacin Najeriya, Sun Halaka Mutane Masu Yawa

Sojoji sun cafke masu taimakon ƴan ta'adda

Ya kuma ce wanda ake zargin da aka kama a Benue, yana karɓar haraji daga mazauna yankin saboda ƴan ta'addan da ke addabar yankin, rahoton Leadership ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A tsakanin 10 zuwa 11 ga watan Oktoba 2023, sojoji sun gamu da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su. Sojojin sun kuma kama wasu masu taimakon ƴan ta'adda guda uku a ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar Borno. Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutanen ukun masu haɗa kai da ƴan ta'adda, sun kasance masu karɓo musu kuɗin fansa."
"Sojojin sun sake hada mutanen biyu da suka gudu daga hannun ƴan ta'addan da iyalansu."
"A ranar 9 ga watan Oktoba 2023, sojoji yayin da suke sintiri na yaƙi sun kama wani dan ta'adda ɗaya a ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue. Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin yana karɓar haraji daga mutanen yankin domin ƴan ta'addan."

Kara karanta wannan

Da Kyau: Dakarun Sojoji Sun Samu Galaba Kan Yan Ta'adda, Sun Tura Masu Yawa Zuwa Barzahu

Ya ƙara da cewa ayyukan da sojoji suka yi a faɗin ƙasar a cikin mako guda da ya gabata ya yi sanadin cafke ƴan ta'adda 95 yayin da aka kashe 37 har lahira.

Za Mu Hukunta Masu Taimakon Yan Bindiga, Gwamna Radda

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin ganin bayan masu taimakon ƴan bindiga a jihar.

Gwamnan ya yi nuni da cewa babu wanda zai saurarawa idan aka same shi da laifin taimakon ƴan bindiga a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng