Kotu Ta Hukunta Wani Mutum Saboda 'Daura Aure' Tsakanin Surukarsa da Buhari
- Kotu ta garkame wani magidanci mai suna Gambo Adamu sakamakon damfarar surukarsa da ya yi
- Kotu ta garkame wani magidanci mai suna Gambo Adamu sakamakon damfarar surukarsa da uya yila aure tsakaninta da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Harma ya kawo mata sadakinta N100,000 da wasu kyaututtuka da ya ce Buhari ne ya aiko da su bayan an daura masu aure
Jihar Neja - Wata kotun majistare da ke zama a Minna, jihar Neja, ta yanke wa wani mutum mai suna Gambo Adamu hukuncin watanni 12 a gidan yari kan kulla auren bogi tsakanin surukarsa, Sa'adatu Aliyu da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wacce ke karar, wacce ta kasance bazawara, ta tunkari kotun cewa surukinta ya karbi kudade daga hannunta wanda ya kai naira miliyan 5 bisa alkawarin hada ta aure da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.
Yadda wani mutum ya gabatarwa surukarsa sadakin aurenta da Buhari
Ta fada ma kotun cewa surukinta ya gabatar mata da N100,000 a matsayin sadaki, da kwandon goro da soyayyiyar kaza a cikin wata jaka a matsayin kyauta daga Shugaban kasa Buhari a yayin daurin auren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa bayan zaman jiran ganin tsohon shugaban kasar ya zo daukarta a matsayin sabuwar amaryarsa, sai ta yanke shawarar tunkarar kotu domin ta shiga lamarin.
Matar ta kara da cewar mai laifin ya kuma bukace ta da ta kafa wata kungiya mai zaman kanta da ita a matsayin shugaba, yayin da shi surukin nata zai zamo kakakin kungiyar, inda ya yi mata alkawarin cewa za ta samu alfanu daga wajen gwamnatocin tarayya da na jiha.
Bugu da kari, ya sanar da ita cewar za ta samu kujerun aikin hajji.
Yadda Dalibar UNILORIN Ta Sha Maganin Kwari Bayan Saurayin Da Suka Hadu a Intanet Ya Damfareta N500k
Daily Trust ta kuma rahoto cewa alkalin kotun, Ibrahim Musa Zago, ya yankewa wanda ake karan hukuncin watanni 12 a gidan yari kan samunsa da laifin zamba wanda ya sabawa sashi na 322 na kundin laifuffuka, tare da zabin biyan tarar N100,000.
Ya kuma umarci wanda ake kara da ya biya mai karar kudi naira miliyan 2 a matsayin diyya.
Buhari ya gama mulki, amma yanzu haka rayuwar nadama yake, inji tsohon ministansa Dalung
A wani labarin, tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana rayuwar nadama tun bayan da ya kammala mulki.
Dalung ya yi zargin cewa yan kanzagin Buhari sun ja masa bacin suna da zubewar daraja a idon 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng