Gwamnatin Imo Ta Mika Asibiti Sukutum Ga Coci Don Kula da Shi Yadda Ya Kamata

Gwamnatin Imo Ta Mika Asibiti Sukutum Ga Coci Don Kula da Shi Yadda Ya Kamata

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya mika asibiti sukutum ga wani coci a jihar don kula da kuma gudanar da asibitin
  • Kwamishinan lafiya a jihar, Dakta Prosper-Ohayagha Success shi ya mika makullan asibitin ga babban Fasto Rabaran Chidi Collins
  • Kwamishin ya ce an dauki wannan mataki ne ganin cewa masu addinin sun fi tsoron ubangiji da kuma tausayin al’umma

Jihar Imo – Gwamnatin jihar Imo ta damka wa wani cocin Anglican da ke Ohaji/Egbema asibiti sukutum don kula dashi.

Kwamishinan lafiya a jihar, Dakta Prosper-Ohayagha Success shi ya mika asibitin ga cocin karkashin jagorancin Rabaran Chidi Collins.

Gwamnan Imo ya mallakawa coci asibiti don ba shi kulawa na musamman
Gwamnatin Imo Ta Mika Asibiti Sukutum Ga Coci. Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: UGC

Meye dalilin mika asibitin ga coci a Imo?

Kwamishinan ya mika cocin ne a ranar Litinin 16 ga watan Oktoba inda ya ce sun mallakar wa cocin asibitin mai dauke da gadaje 42, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Duniya Ta Yi Tir da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 Kwance a Asibiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Success ya ce gwamnan jihar ya dauki wannan matakin ne saboda asibitin zai fi samun kulawa a hannun masana addinin kuma masu tsoron ubangiji.

Ya ce:

“Gwamnan ya yi hikimar haka ne ganin cewa zai fi kyau a bai wa masu addinin kula da asibitin saboda za su nuna tausayawa ga marasa lafiya da kuma kula da asibitin sosai.”

Ya kara da cewa akwai wani asibiti irinsa da aka gina a kananan hukumomin Oguta da Oru ta Gabas wadanda za a mika su ga cocin su ma don tabbatar da ba su kulawa na musamman, AllNews ta tattaro.

Wane martani Faston cocin ya yi a Imo?

Kwamishinan ya ce Fastoci na da sinadarin waraka a kansu idan har su ke kula da asibitin to za a samu abin da ake nema na waraka inda ya ce dole su zabo mai gaskiya saboda asibitin na yankin karkara ne.

Kara karanta wannan

Kano: An Kama Mutum 30 Kan Yunkurin 'Tayar da Tarzoma' a Wurin Auren Gata 1,800, Sun Yi Bayani

Ya kara da cewa:

“Idan ka damka irin wannan babban aiki a hannun wasu mutane, ba za a samu kudaden da asibitin ke kawo ba.”

Yayin da ya ke karbar makullan asibitin, Rabaran Chidi Collins ya godewa gwamnan da daukar mataki irin wannan inda ya bai wa coci don kula da asibitin.

INEC ta nuna damuwa kan yanayin tsaro a Imo

A wani labarin, Hukumar zabe ta INEC ta nuna damuwa kan yanayin tsaro a jihar Imo gabanin zaben da za a gudanar.

Hukumar ta nuna damuwar ce yayin da ta ke shirye-shiryen gudanar da zabe a watan Nuwamba mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.