Yan Bindiga Sun Hallaka Mataimakin Magatakardar Kwaleji a Jihar Imo
- Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin mataimakin magatakardar Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke jihar Ebonyi
- Maharan sun kai farmakin ne a gidan Innocent Obi a karamar hukumar Ehime Mbano da ke jihar Imo
- Marigayin wanda aka fi sani da 'Onye Army' ya yi ritaya a aikin soja kafin ya koma aiki a Kwalejin Gwamnatin Tarayya
Jihar Imo - 'Yan bindiga sun yi ajalin mataimakin magatakardar Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Uwana a jihar Ebonyi.
Marigayin mai suna Innocent Obi ya rasa ransa ne a jihar Imo yayin da maharan su ka afka mishi a yankin Umuezeala da ke karamar hukumar Ehime Mbano, cewar Vanguard.
Waye 'yan bindigan su ka kashe a Imo?
Ana zargin masu rajin kafa kasar Biafra ne wanda su ke cin karensu ba babbaka a yankin Kudu maso Gabashin kasar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi wanda aka fi sani da 'Onye Army' ya yi ritaya a aikin soja kafin fara aiki a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Uwana.
Maharan wadanda sun kai mutum shida cikin shigar jami'an tsaro sun afka gidan Obi ne da misalin karfe 10 na dare inda su ka ta da hankulan jama'a.
Ta yaya aka hallaka Obi a Imo?
Wata majiya ta tabbatar da cewa:
"Sun balla kofar gidansa inda su ka farmasa da sara da adda da kuma gatari, ya yi ihu mutane sun kawo dauki amma matasan su ka fara harbi a sama.
"Hakan ya sanya mutane guduwa inda su ka tafi da Obi, 'yan sa kai sun bazama nemanshi amma ba a gan shi ba.
"Sai bayan kwana biyu aka samu gawarsa kwance da sara yadda ba za ka iya gane shi ba."
An bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda duk matashin da ke son karatu zai sama mishi gurbin karatu a makarantar.
Majiyar ta ce Obi mutum ne mai kan-kan da kai wanda ba ruwansa da shiga harkar mutane kuma ba ya nuna kansa.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon soja a Imo
A wani labarin, Masu garkuwa sun sace wani tsohon soja a karamar hukumar Owerri ta Arewa a jihar Imo.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun yi nasarar sace Mista Richard Duru ne bayan sun yi masa kwanton bauna.
Asali: Legit.ng