‘Yan Majalisa Sun Bukaci a Gaggauta Bude Iyakar Nijar Duk da Takunkumin ECOWAS

‘Yan Majalisa Sun Bukaci a Gaggauta Bude Iyakar Nijar Duk da Takunkumin ECOWAS

  • ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun tattauna a game da iyakokin Najeriya da su ka shafe tsawon lokaci su na a rufe
  • A zaman da su ka yi a farkon makon nan, ‘yan majalisar sun yarda a bude iyakokin Najeriya-Nijar da aka garkame
  • Majalisar ba ta goyi bayan sake bude sauran iyakokin Kudu da aka rufe a lokacin Muhammadu Buhari ya na ofis ba

Abuja – Bayan dogon lokaci a rufe, majalisar wakilan tarayya ta nemi gwamnatin tarayya ta sake bude iyakokinta da kasar Jamhuriyyar Nijar.

The Cable ta ce ‘yan majalisar tarayya su na so a bude duka iyakokin da ke garuruwan Maigatari, Mai’Aduwa, Kongwalam da kuma Illela.

Aliyu Sani Madakin Gini mai wakiltar Dala a majalisar wakilai, ya bijiro da batun a ranar Talata.

Majalisar wakilai
Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Gwamnati ta rufe iyakar jamhuriyyar Nijar

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

Tun watan Agustan nan gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta da makwabciya Nijar sakamakon juyin mulki da sojoji su ka yi a jamhuriyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum ya jawo kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ta sa aka kakabawa Nijar takunkumi.

'Yan kasuwan Arewa su na asara

Honarabul Aliyu Sani Madakin Gini wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye ya nuna muhimmancin kasuwancin da ake yi.

‘Dan majalisar ya ce mutanen Arewa su na samun ciniki sosai tsakanin al’ummar Nijar, Mali, Chad da Kamaru a Maigatari, Kongwalam da Illela.

Premium Times ta ce ‘dan majalisar na Kano ya ce rufe iyakokin ya jawo kiyayya tsakanin wadannan al’umma da ke makwabtaka da juna.

Ka da a bude iyakokin da ke kudu

A dalilin matakin da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka, Hon. Aliyu Sani Madaki ya nuna cewa an samu karuwar fasa kauri da sauran laifuffuka.

Kara karanta wannan

An Bayyana Ainihin Dalilin da Ya Sanya Wike Ya Gana da Bukola Saraki

Abin da ‘yan majalisar su ka amince a kai shi ne a bude iyakokin da ke Arewa, amma a rika sa ido, sannan ba a yarda da bude iyakokin da ke kudu ba.

Bola Tinubu ya nada mukamai

Dazu ne labari ya zo cewa shugaba Bola Tinubu ya umarci Ahmed Galadima Aminu ya hau kujerar rikon kwarya a PTDF kafin ya fara wa’adinsa.

Nadinsa ya biyo bayan murabus da Shugaba mai barin gado, Bello Aliyu Gusau ya yi a karshen Satumba, hakan ta sa aka dauko Galadima Aminu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng